Bayanai da muke samu daga jamhuriya Nijar na nuni da cewar shugaban 'yan adawa da shugaban majalisar dokoki sun aikewa shugaban kasar da wata wasika inda suka bukace shi daya kira taron gagawa na majalisar datijan kasa da ake kira ''conseil de la republique'' don shawo kan matsalar rikicin siyasa da ake fuskanta a kasar. Wanan wasikar dai ta biyo bayan irin cece-kucen da ake fuskanta yau kusa da makwani uku danganeda rigingimun siyasa da ake fuskanta a kasar ta Nijar. yanzu haka dai A jamhuriya Nijar batun da ya fi daukan hankulan jama'a shine rikicin cikin gida da ake fuskanta a babbar hukuma ta biyu ta kasar wato majalisar dokoki inda yanzu haka dai 'yan majalisar dokoki na bangaren adawa da masu rinjaye suka kasa fahimtar juna akan nada mataimakin shugaban majalisar dokoki na biyu. Tuni dai wasu majiyoyi daga kasar ta Nijar suka ambata cewar harkoki sun saya cik a zaman majalisar dokokin kasar na farko a bana.ABNA.
3 Mayu 2014 - 17:07
Lambar labari: 606343
Nijar : An Bukaci Shugaba Issufu Ya Kira Taro Gagawa Kan Rigingimun Siyasa