Da safiyar ranar Asabar, 22 ga Agusta 2026, Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) ya rufe taron ɗaliban Firamari da Sakandire na IVC a Abuja, wanda Dandalin Ɗaliban Harkar Musulunci ke shiryawa a duk lokacin hutun yara.
Cikin daren yau Talata 29 ga Almuharram 1448 (14/7/2026), Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya gana da 'yan uwa almajiransa da suke karatu a Hauzozin Karbala mai tsarki a ƙasar Iraq.
Sheikh Ibrahim Zakzaky ya shigo Najaf Ashraf don halartar jana'izar gawar Shahidin Jagoran al'umma. An shirya cewa bayan ganawa da tattauna da malamai da shugabannin addinai na Iraki, zai tafi Mashhad mai tsarki don halartar taron binnewa.