6 Agusta 2026 - 17:54
Source: ABNA24
Gaza: Keta Tsagaita Wuta; Hare-haren Sojojin Isra'ila Na Ci Gaba A Yankuna Daban-daban Na Zirin Gaza

A daidai lokacin da ake ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wuta, sojojin Isra’ila, ta hanyar harba manyan bindigogi, harba makaman atari, da kuma ci gaban kutsawar soji a yankuna daban-daban na zirin Gaza, sun sake kai hari ga wuraren masaukin 'yan gudun hijira; hare-haren da suka yi sanadin raunata aƙalla Bafalasdine ɗaya da kuma ƙara damuwa mazauna waɗannan yankuna.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) - ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Majiyoyin gida sun bayyana cewa sojojin Isra’ila a yau (Alhamis) sun kai hari ta hanyar harbin bindigogi da makaman a yankuna daban-daban na kudu da tsakiyar zirin Gaza, ciki har da yankin al-Mawasi a Khan Younis.

A cikin waɗannan hare-haren, wani Ba’Falasdine ya jikkata, kuma sun ci gaba da harba manyan bindigogi a kan tantunan 'yan gudun hijira a wurare da dama. Haka nan yankunan gabashin Khan Younis sun fuskanci harbin makamai, kuma a lokaci guda an harba harsasai masu haske a saman waɗannan yankuna.

A lardin Rafah ma, tankokin sojojin Isra’ila sun bude wuta kan wurin da ake tsugunar da 'yan gudun hijira a yankin al-Mawasi, kuma a lokaci guda motocin sulke na wannan gwamnatin sun wuce iyakar abin da ake kira "layin rawaya."

A tsakiyar zirin Gaza ma, arewacin sansanin al-Bureij ya fuskanci harbin bindigogi da yawa da motsin soji, wanda ya sa mazauna suka tsaya a gidajensu da wuraren zamansu.

Ma'aikatar lafiya ta Falasdinu a Gaza ta sanar a cikin sabbin abubuwan da suka faru, an fitar da gawarwakin shahidai biyu daga ƙarƙashin gine-ginen da ka rusa, kuma wasu biyu da suka jikkata a baya sun shahada.

Har ila yau, an kai wani sabon wanda yaji rauni zuwa asibiti. Wannan ma'aikatar ta kara da cewa har yanzu wasu daga cikin wadanda abin ya shafa suna ƙarƙashin baraguzan gine-gine ko kuma a yankunan da ba a iya isa ba, kuma ma'aikatan agaji ba su da damar isa gare su.

Bisa ga ƙididdigar ma'aikatar lafiya ta Falasdinu, tun lokacin da aka fara aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta zuwa yanzu, sakamakon hare-haren ta’addancin Isra’ila da aka yi wa wannan yarjejeniya, Falasdinawa 1,254 ne sukai shahada, kuma 4,121 suka jikkata. Har ila yau, adadin shahidan yaƙin Gaza daga 7 ga Oktoba 2023 zuwa yanzu ya kai 73,381, kuma adadin wadanda suka jikkata ya kai 174,231.

………..

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha