Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) - ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Mai magana da yawun sojojin Iran a yau Talata ya bayyana cewa "Sojojinmu ba za su ja da baya ko kaɗan game da mashigar Hurmuz ba," ya kara da cewa "ba za a sake bude mashigar Hurmuz ta hanyar yaƙi da munanan motsi da ta'addancin Amurka ba".
Ya kuma ci gaba da cewa "hanya ɗaya tilo don sake bude mashigar Hurmuz ita ce mutunta haƙƙoƙin al'ummar Iran," ya kara da cewa "muna da alhakin neman fansar jinin shahidanmu musamman Imam Shahid Sayyid Ali Khamene'i".
………………………….
Ra'ayinka