14 Yuli 2026 - 23:09
Source: ABNA24
Yemen: Na Ci Gaba Da Ragargazar Saudiyya Da Makamai Masu Linzami

Amurka da gwamnatin yahudawa masu mamaya, saboda rashin iyawarsu wajen fuskantar Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kawayenta a yankin, sun ba da umarni ga masarautun wahabiyawa a yankin da su shirya hare-hare a kan Iran da Yemen. Trump ya yi magana game da wannan a jawabinsa na jiya.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) - ABNA – ya bayar da rahoton cewa: A cewar kafofin yada labarai na yankin, an harba makamai masu linzami da dama daga Yemen zuwa filin jirgin sama na Abha na gwamnatin wahabiyawan Saudiyya.

Bayan harin Yemen, an dakatar da dukkan jiragen sama a filin jirgin sama na Abha na Saudiyya gaba daya.

Haka kuma an ba da rahoton cewa an ji karar fashe-fashe a jere a birnin Asir na Saudiyya.

Gwagwarmayar musulunci ta Yemen ta bayyana waɗannan hare-hare a matsayin martani ga ta'addancin Saudiyya.

Sojojin Yemen sun sanar da cewa sun sami nasarar kakkabo wani jirgin saman leke asiri nau'in "Wing Loong 2" na Saudiyya, a lokacin da yake gudanar da ayyukan liken asiri da safiyar yau a sararin samaniyar lardin Al-Bayda a tsakiyar ƙasar, inda suka kai masa hari da makamin da ya dace kuma da iko da yardar Allah sun kakkabo shi.

Sojojin a cikin wata sanarwa da Birgediya Janar Yahya Saree ya buga, sun tabbatar da cewa suna shirye kuma za su kasance a faɗake ga duk wani keta sararin samaniya da ikon ƙasar, kuma ba za su tsaya suna kallo duk wani ta'addanci ba, sun dogara ga Allah kuma sun yin amanna da shi.

Ya kamata a lura cewa Amurka da gwamnatin yahudawa masu mamaya, saboda rashin iyawarsu wajen fuskantar Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kawayenta a yankin, sun ba da umarni ga masarautun wahabiyawa a yankin da su shirya hare-hare a kan Iran da Yemen. Trump ya yi magana game da wannan a jawabinsa na jiya.

Tunatarwa: Yau A Duniyar Musulunci A Babbar Kasar Musulunci Amma Kafirai Ne Ke Sanya Shugabannin Kasar Musulumi Kai Hari Kan Wata Kasa Yar Uwarta Musulma Wannan Wane Irin Yanayi Ne Mu Ke Ciki, Kum Aga Wata Kasa Musulma Tana Yaki Da Kasa Kafira Amma Sauran Kasashen Musulmi Sun Kit Ay Ta Sai Dai Ma Su Hada Kai Da Kasar Kafirai Suna Mata Zagon Kasa Ku Bayyana Mana Ra’ayinku

…………….

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha