Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya bayar da rahoton cewa: A gab da taron tarihi na jana'izar gawar jagora shahidi, an gudanar da taron na musamman mai taken "Gadon Dabaru da Wayewa na Jagora Shahidin Al'umma" tare da halartar wasu manazarta biyu fitattu daga Yemen da Bahrain. A wannan taron da aka keɓe don nazarin fannonin da suka fice na tunani da rawar wayewa da tasirin jagora shahidin al'umma a yankin gabas ta tsakiya da ma duniya baki daya, masana sun yi nazarin dalilin da ya sa masu girman kai da gwamnatocin da ke dogara ga kasashen waje ke tsoron yaɗuwar jawabinsa a kasashe kamar Yemen da Bahrain.
Wanda Kamfanin Dillancin Labarai na ABNA ya karbi bakuncinsa, tare da jawabin Dr. Issam al-Amad, masani dan Yemen mai binceke, da Dr. Rashid al-Rashed, mai fafutukar siyasa na Bahrain, a dakin taro na wannan kamfanin dillancin labarai.
Juyin Juya Halin Al'adu da Siyasa Bayan Shahadar Jagoran Juyin Juya Hali
Dr. Issam al-Amad, masani kuma mai bincike dan Yemen, a wannan taron, yayin da yake yaba da girman yanayin jagora shahidin juyin juya hali, ya bayyana cewa shahadarsa na iya haifar da "juyin juya halin al'adu da siyasa" a duniyar bil'adama, kuma ya yi hasashen cewa jana'izarsa za ta zama wani babban lamari da zai jawo hankalin duniya sama da duniyar Musulunci.
Sallar Jana'iza Ga Wanda Ya Ke Nesa A Duk Faɗin Duniya
Dr. al-Amad ya kuma ba da shawarar cewa don yaɗa wannan lamari a matakin duniya, limaman sallah a kasashe daban-daban - musamman a tsakanin Ahlus-Sunnah da Zaidiyyah waɗanda suke halasta da sallar jana'iza ga wanda yak e nesa - su yi sallar jana'iza ta Ga’ib a daidai lokacin da ake gudanar da jana'izar, don wannan aiki ya zama wani lamari na duniya wajen yaɗa al'adun shahada.
Dubin Dabaru Na Jagora Shahidi Game Da Fagen Gwagwarmaya; Daga Yemen Zuwa Mashigar Babul-Mandab
A wani bangare na jawabinsa, ya yi nuni ga rawar dabaru na jagoran juyin juya hali a farkawar Musulunci a Yemen, kuma ya bayyana shi a matsayin daya daga cikin mutanen da suka fi tasiri wajen samuwar ƙungiyar Ansarallah, wanda tun shekaru da dama yana da alaƙar tunani da al'adu da shugabanni kamar Badruddin al-Houthi da Sayyid Abdul-Malik al-Houthi. A cewar Emad, jagoran juyin juya hali shekaru da dama da suka gabata, da hangen nesa na abinda zaizo gaba, ya lura da muhimmancin dabaru na mashigar Babul-Mandab, kuma har ma ya ba da umarnin sake gina Makabartar "Nasir Atroush" don ƙarfafa alaƙar al'adu da Yemen.
Ya kara da cewa wannan shahidi mai girma yana da halaye da yawa, kuma tare da saninsa kan al'amuran siyasa da soji da kuma cikakken sanin Amurka da Isra'ila, yana da ƙwarewa sosai a fannonin tarihi, sanin mutane masu daraja, falsafa, sufanci da adabin Farisanci, Larabci da Turkiyya.
Emad ya ci gaba da kwatanta hanyar tafsirin jagoran juyin juya hali da Sayyid Qutb, ya jaddada cewa shi, sabanin wasu ƙungiyoyin Musulunci waɗanda suka fi mayar da hankali ga bangaren siyasa na Alƙur'ani, ya sami damar yin haɗi mai zurfi tsakanin "siyasa da ruhaniya."
Ya kuma yi nuni ga rawar "ƙaunar shahada" a cikin tsarin tunaninsa, ya ce tasirin jinin wannan shahidi ya kai har wasu da suka rabu da ƙungiyoyin tsattsauran ra'ayi har ma da wasu daga cikin 'yan Daesh bayan shahadarsa sun karkata zuwa makarantar Ahlul-Bayt (a.s).
Emad a ƙarshe ya yi ishara da cewa a yau mutanen Yemen da yawancin Musulmai na duniya, ban da Lura da ra'ayoyin siyasa na jagoran juyin juya hali, suna da sha'awar sanin zurfin tushen tunaninsa a batutuwa kamar Mahdawiyya da tarihin Imamai Tsarkaka.
Tushen Da Ya Haɗu Da Iran; Ƙalubalen Al Khalifa Ga Wilayat Al-Faqih
A wannan taron, Dr. Rashid al-Rashed, daya daga cikin shugabannin yunkurin addinin Musulunci a Bahrain, ya bayyana rashin jagora shahidin juyin juya halin Musulunci a matsayin wata asara da ba za a iya maye gurbinsa ba ga dukan duniyar Musulunci.
Yana mai nuni ga matsayin Marja’iyyah da jagoranci na wannan shahidi, ya bayyana shi a matsayin mai zaburantarwa ga matasa da ƙungiyoyin gwagwarmaya a yankin ciki har da Lebanon, Iraqi, Yemen da Bahrain, ya kara da cewa a lokuta masu muhimmanci, maganarsa da matsayinsa sun kasance jagora ga yunkurin masu imani.
Wannan mai fafutukar siyasa na Bahrain, yayin da ya jaddada alaƙar tarihi da asali mai zurfi tsakanin Bahrain da Iran, ya bayyana cewa fiye da rabin mutanen Bahrain asalinsu Iran ne, kuma wannan ƙasa ba ta da wata alaƙar asali da Saudi Arabiya.
A bayanins yayi kakkausar suka ga gwamnatin Al Khalifa, inda ya bayyana ayyukan danniya na wannan gwamnati a kan malamai, mawaƙan addini na Bahrain a matsayin tsoron masu mulki daga tasirin jagorancin addini da siyasa na jagoran juyin juya hali a tsakanin jama'a.
Dr. Rashid al-Rashed ya ci gaba da jaddada cewa gwamnatin Al Khalifa tana ɗaukar "Wilayatul-Faqih" a matsayin laifin siyasa, kuma ta hanyar kama malamai da dama, tana ƙoƙarin danne koyi da addini na jama'a daga jagorancin addini na Iran.
A cewar Dr. al-Rashed, Al Khalifa ta ma takaita taruka domin Imam Husaini da taron Ashura a kan zargin yaɗa jagorancin Wilayatul-Faqih, amma waɗannan matsin lamba ba su iya yanke haɗin zuciya da imani na mutanen Bahrain ga jagoranci da wayewar Iran, kuma wannan gadon tunani zai ci gaba da zama jagorar hanyarsu.
…………………..
Your Comment