29 Yuni 2026 - 19:27
Source: ABNA24
Shin Somaliland Bangare ne na Lissafin Bahar Maliya? Ana Tattauna Sabon Matakin Isra'ila

Ana hasashen cewa matakin da Isra'ila ta ɗauka na amincewa da Somaliland, ba yanke shawara ta diflomasiyya kaɗai ba ce, a'a, tana cikin wani lissafi mai zurfi na siyasar duniya (geopolitical) na dogon lokaci, wanda ke nufin kafa tasiri a mashigar Babul-Mandab da kuma Bahar Maliya.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya bayar da rahoton cewa: Ana kallon matakin da Isra'ila ta ɗauka na amincewa da Somaliland a matsayin wani ci gaba mai ban sha'awa dangane da daidaiton siyasar duniya a yankin. A cewar sharhin da ake yadawa a ma'aikatun diflomasiyya, wannan shawarar na iya wuce amincewa ta alama kawai, ta zama wani bangare na dabarun ƙara karfin tasiri a yankin Bahar Maliya.

Masana suna nuni da cewa mashigar Babul-Mandab tana da matukar muhimmanci ga harkokin kasuwanci na duniya. Wannan hanyar ruwa mai kunkuntar da ke haɗa Bahar Maliya da Tekun Aden, ana kallonta a matsayin hanya mai muhimmanci da yawancin jigilar kayayyaki ta ruwa tsakanin nahiyar Turai da Asiya ke ratsawa ta magudanar Suez. Don haka, dangantakar diflomasiyya da ta soji da ake ginawa a wannan yanki, ba wai tana shafar daidaiton cikin gida kawai ba ne, har ma tana tasiri ga daidaiton kasuwancin duniya baki ɗaya.

Somaliland kuma, saboda yanayin wurinta na nahiya, ta kasance kusa da wannan layi. Wannan yanki da ba ya da cikakkiyar amincewar duniya, a shekarun baya-bayan nan yana ƙoƙarin ƙara dangantakarsa ta tattalin arziki da diflomasiyya da wasu ƙasashe. Ana la'akarin cewa matakin da Isra'ila ta ɗauka a cikin wannan tsari na iya zama wani sabon mataki ta fannin diflomasiyya da dabaru a kahon Afirka.

Manazarta da ke lura da al'amuran yankin suna bayyana cewa gwamnatin Tel Aviv tana neman sabbin damammaki a fannoni kamar tsaron hanyoyin jigilar kayayyaki ta ruwa, hadin gwiwar leƙen asiri, da kuma samun hanyoyin kayan aiki. Ƙaruwar hadurran tsaro a layin Bahar Maliya da barazana ga hanyoyin kasuwanci sun sa wannan yanki ya zama ɗaya daga cikin wuraren da ake fafatawar karfin iko na duniya.

A gefe guda, gwamnatin Somaliland tana nanata cewa samun amincewar duniya yana da matukar muhimmanci ga ci gaban tattalin arzikinta da kwanciyar hankalin siyasarta. Sai dai har yanzu ba a fayyace yadda ƙungiyar Tarayyar Afirka da sauran ƙasashen yankin za su karɓi wannan ci gaba ba.

A cewar masana, wannan matakin ba kawai zai kawo sabuwar dangantakar diflomasiyya tsakanin ɓangarorin biyu ba ne, har ma zai iya haifar da sabbin muhawara game da daidaiton siyasar duniya da ke faruwa a kewayen Bahar Maliya da mashigar Babal-Mandab. Don haka, za a sa ido sosai kan tasirin wannan ci gaba a kan ƙawancen yanki da manufofin tsaron ruwa a nan gaba.

................................

Your Comment

You are replying to: .
captcha