Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya bayar da rahoton cewa: Sojojin gwamnatin yahudawa da yammacin ranar Litinin sun sanar da cewa wani sojan wannan gwamnati ya ji mummunan rauni sakamakon wata fashewa a kudancin Lebanon.
A cikin sanarwar sojojin gwamnatin yahudawa yazo cewa: Wani sojan ajiya na yahudawa a yau Litinin ya ji mummunan rauni sakamakon fashewar abu a kudancin Lebanon.
Sojojin gwamnatin yahudawa sun kara da cewa an kai wannan sojan asibiti domin samun kulawar lafiya, kuma an sanar da iyalansa game da halin da yake ciki.
Sojojin gwamnatin yahudawa ba su fitar da ƙarin bayanai game da yanayin wannan fashewa ba, amma tashar talabijin ta 12 ta wannan gwamnati ta ruwaito cewa wannan sojan ya ji rauni ne a yayin wani aiki na sojojin rundunar kwamando a garin "Arnon" da ke cikin gundumar Nabatiyah a kudancin Lebanon.
Wannan tashar ta kara da cewa: Har yanzu ba a san menene tushen fashewar ba, kuma ana ci gaba da binciken yanayin lamarin.
Tun da farko, sojojin gwamnatin yahudawa a jiya Lahadi sun sanar da mutuwar wani hafsa mai mukamin Kyaftin da kwamandan wani sashe a bataliya ta 12 ta Golani, da kuma raunatar wani soja a yayin wani rikici a kudancin Lebanon.
Ci gaba da Boye Bayanai Game da Asarar Gwamnatin Yahudawa
Gwamnatin yahudawa a lokacin yaƙe-yaƙe da ayyukanta na soji a Lebanon da sauran yankuna, tana sanya labule mai tsanani kan yaɗa bayanai game da asarar rayuka da barnar dukiya.
Saboda haka, wasu majiyoyi sun yi imanin cewa alkaluman hukuma da ake bayyanawa game da barnar da asarar na iya ƙaruwa nan gaba.
……………………………
Your Comment