Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: rikicin soji tsakanin Amurka da Iran a kwanakin baya ya fuskanci wani juyi na kwatsam da ba ai zato ba. Domin Donald Trump, shugaban Amurka, bayan kwanaki na yin barazana mai tsanani ga Iran da gargadi game da kai hare-hare da yawa a cikin ƙasar da kuma kwace muhimman cibiyoyin man fetur, ya sauya tafarkinsa inda ya yi magana game da cimma wata babbar yarjejeniya ta siyasa don kawo karshen yakin.
Bisa rahoton Cibiyar Watsa Labarai ta Aljazeera, lamarin ya fara ne lokacin da Trump a ranar Alhamis da ta gabata a cikin wani sako a shafinsa na sada zumunta, ya dauki matsayi mai tsauri kan Iran, yana mai barazanar cewa Amurka na iya kai hare-haren soji masu tsanani a kan kasar. Ya kuma yi magana game da yiwuwar kwace cikakken iko da tsibirin Kharak, daya daga cikin muhimman cibiyoyin fitar da man Iran a cikin Tekun Farisa. Matakin da zai iya haifar da sakamako mai yawa ga kasuwar makamashi ta duniya.
Sanarwa Ƴar Burun-burun Game Da Yarjejeniya Ta Kusa
Kamar yadda jaridar New York Times ta rubuta, wadannan barazanar sun zo ne bayan kwanaki biyu na gwabza kazamin fada ta hanyar makamai masu linzami da na sana tsakanin sojojin Amurka da na Iran. Fadace-fadacen da suka tsananta bayan da aka harbo wani jirgin sama mai saukar ungulu na Amurka nau'in Apache wanda hakan ya kara fargabar yankin game da rikicin da ke canjawa zuwa babban yaki a Gabas ta Tsakiya.
Amma sa'o'i kadan bayan wannan lamari, Trump ya bi wata hanya ta daban ya kuma sanar da cewa an soke hare-haren da aka shirya a kan Iran. Ya bayyana dalilin wannan kudirin a matsayin ci gaban tattaunawa da jami'an Iran da kuma cimma fahimtar juna na farko tsakanin bangarorin biyu.
Trump a cikin taron manema labarai da ya yi a fadar White House ya ce: "An cimma wata fahimtar juna ta farko, ana ci gaba da matakan karshe na tsara ta, kuma mai yiwuwa a sanya hannu a kanta a daya daga cikin kasashen Turai a kwanaki masu zuwa."
Ya bayyana wannan yarjejeniya a matsayin babbar fahimtar juna mai karfi, kuma ya yi iƙirarin cewa wannan yarjejeniya za ta iya kawo karshen yakin da ya fara tun daga ranar 9 ga watan Maris, 2025 tare da hare-haren hadin gwiwa tsakanin Amurka da kuma kasar Isra'ila a kan Iran.
Duk da haka, Tehran ta musanta labarin Amurka game da cimma yarjejeniya ta karshe. Ismail Baqaei, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ya bayyana cewa ikirarin da ake yi game da yarjejeniya har yanzu ba su wuce hasashe ba, kuma ba a tantance wani batu ba bisa kafaffen tsari.
Ya jaddada cewa an duba sassa da yawa na rubutun tattaunawar, amma Iran ba ta kai ga sakamako na karshe ba, kuma ba za ta ketare jajaye layukanta ba.
Kyakkyawan Fatan Trump Da Shakku Kan Gaskiyar Tattaunawar
A kan haka, Niall Stanage, manazarcin jaridar The Hill, ya rubuta cewa Trump tun lokacin da aka fara yakin da ake yi wa Iran, ya sha magana game da kusancin yiyuwar yarjejeniya, amma bambancin wannan karon shi ne, ya yi magana game da takamaiman lokacin sanya hannu kan yarjejeniyar da kuma goyon bayan kasashen yankin ga tsarin tattaunawar.
A cewar Trump, wannan yarjejeniya tana samun goyon bayan kasashe kamar Saudiyya, UAE, Qatar, Turkiyya, Pakistan, Bahrain, Kuwait, Jordan, da Masar.
Duk da haka, wasu manazarta sun yi imanin cewa kyakkyawan fata da Trump ya nuna bai dace da yawan rashin fayyacewa da ke tattare da yarjejeniyar ba. Domin har yanzu ba a san makomar shirin nukiliyar Iran, tarin uranium da aka inganta, da kuma yuwuwar takunkumai a wannan fanni ba.
Jaridar The Hill ta kuma yi nuni da cewa Benjamin Netanyahu, firaministan kasar Isra'ila, ya bayyana cewa kasar tasa ba ta goyon bayan wannan fahimtar juna, kuma duk wata yarjejeniya ta karshe dole ne ta hada da fitar da uranium da aka inganta daga Iran, ruguza cibiyoyin sarrafa uranium, takaita shirin makamai masu linzami na Iran, da kuma kawo karshen goyon bayan Tehran ga kungiyoyi masu dauke da makamai a yankin.
Wannan matsayi na nuna cewa yawancin batutuwa masu muhimmanci tsakanin bangarorin har yanzu ba a warware su ba, kuma abin da aka gabatar, mafi yawa wani tsari ne na farko don ci gaba da tattaunawa.
Martanin Kasuwannin Duniya Ga Labarin Yuwuwar Yarjejeniyar
Bangaren tattalin arziki, kalamai masu kyautata zato na Trump game da yuwuwar cimma yarjejeniya, sun haifar da martani mai kyau nan take a kasuwannin kudi na duniya.
Kamar yadda Niall Stanage ya rubuta, manyan ma'aunin hannayen jari na Amurka sun karu bayan fitowar wannan labari. Ta yadda ma'aunin masana'antu na Dow Jones da ma'aunin S&P 500 suka karu da kusan kashi biyu cikin dari, sannan ma'aunin fasaha ya karu da fiye da kashi biyu da rabi cikin dari.
Wannan karuwar darajar kasuwanni ta samu ne mafi yawa saboda fatan sake bude mashigar Hormuz da kuma kawo karshen takunkumin teku na Amurka kan hanyoyin da ke da alaka da Iran. Batu ne wanda a makonnin da suka gabata ya haifar da fargaba mai yawa game da tashin farashin mai a kasuwannin duniya.
Tun lokacin da aka fara yakin da ake yi wa Iran, farashin man fetur ya karu da kusan kashi 30 cikin dari, kuma fargabar dagula fitar da makamashi daga yankin Tekun Fasha, ta kasance daya daga cikin muhimman abubuwan da ke matsa lamba kan tattalin arzikin duniya.
Yunkurin Yanki Don Hana Tsananta Rikici
Gidan yanar gizon Politico a cikin wani rahoto na musamman ya bayyana cewa ja da baya da Trump ya yi kwatsam daga zabin soji, ba shawara ce ta kwatsam ba, sai dai sakamakon kokarin diflomasiyya mai tsauri da shugabannin yankin suka yi don hana fadada yakin.
Dangane da wannan rahoton, kiran gaggawa tsakanin manyan jami'an yankin da Trump ya taka muhimmiyar rawa wajen sauya tsarin Amurka.
Daga cikin wadannan kiraye-kirayen akwai tattaunawar sarki Qatar, shugaban UAE, da kwamandan sojojin Pakistan da shugaban Amurka. Wadannan jami'an sun yi kokarin shawo kan Trump cewa hanyar tattaunawa har yanzu tana da yuwuwar yin nasara.
A cewar jami'an Amurka da jami'an diflomasiyyar da suka yi magana da wannan kafar yada labarai, wadannan shawarwari sun sa Trump ya dakatar da aiwatar da harin soji, kuma ya ba da damar ci gaba da tsarin diflomasiyya.
Dangane da rahoton wannan kafar yada labarai, fahimtar juna da aka gabatar a halin yanzu ya fi mayar da hankali kan sake bude mashigar Hormuz da kawo karshen takunkumin teku masu alaka da Iran, yayin da batutuwa masu sarkakiya kamar shirin nukiliyar Iran za a yi nazari a kan su a tattaunawar gaba.
An kuma bayyana cewa Washington da Tehran sun tattauna game da yiwuwar sakin wani bangare na kadarorin kudi na Iran da aka killace a Qatar da wasu kasashe. Wadannan kadarorin da aka kiyasta darajarsu ta haura dala biliyan 16, za su iya rage matsin tattalin arziki kan Tehran.
Duk da wadannan alamun, har yanzu akwai shakku da yawa game da matsayin karshe na shugabannin Iran. Wani jami'in diflomasiyyar Larabawa a cikin tattaunawa da Politico game da yuwuwar aiwatar da yarjejeniyar ya ce: "Lokacin da na ga ta tabbata ne zan yarda da faruwarta".
Gargadi Game Da da Hukuncin Gaggawa
Jaridar New York Times ta nakalto daga Pete Hegseth, ministan tsaron Amurka, inda ta rubuta: "Idan dole ne mu yi tattaunawa da bam, za mu yi tattaunawa da bam."
Wadannan kalamai na nuna tsarin hari na gwamnatin Amurka kafin canjin hanya kwatsam kan batun tattaunawa da Iran.
A daya bangaren, Mohammad Baqer Qalibaf, shugaban tawagar masu tattaunawa ta Iran, ya yi gargadin cewa hukunce-hukuncen gaggawa na iya dagula al'amura, su jefa har kar makamashi da kasuwanni cikin hadari, da kuma jefa yankin cikin wani dogon rikici.
A Amurka kuma, batun yuwuwar yarjejeniya da Iran ya fuskanci martani daban-daban. Wasu 'yan majalisa sun bukaci yin nazari mai zurfi kan kowace yarjejeniya.
Lindsey Graham, sanata mai ra'ayin Republican, ya bayyana cewa yana fatan za a cimma yarjejeniya ta hakika kuma mai tushe, wacce za ta sha banban da yarjejeniyar nukiliya ta lokacin shugabancin Barack Obama, kuma duk wata sabuwar yarjejeniya za a gabatar da ita ga majalisa don nazari.
Shakku Game Da Sakamakon Amfani Da Karfin Soji
Wasu masana sun yi imanin cewa yin amfani da karfin soji don matsawa Iran zai iya haifar da sakamako mara kyau.
Riccardo Alcaro, wani mai bincike dan Italiya, a kan haka ya ce: "Idan Iran ta ji cewa ana amfani da karfin soji ne don tilasta mata abubuwan da ba za ta amince da su ba, mai yiwuwa a maimakon ja da baya, za ta zabi hanyar gwagwarmaya ne."
Duk da kyakkyawan yanayin da Trump ya yi kokarin haifarwa ta hanyar sanar da babbar yarjejeniya, rashin samun rubutun yarjejeniya na karshe da kuma ci gaba da sabani game da shirin nukiliyar Iran, takunkumai, da kuma batutuwan tsaro na yankin, yana nuna cewa yin magana game da wani canji na tarihi har yanzu bai tabbata yi ba.
Ko da yake shiga tsakanin kasashen yankin ya yi nasarar hana samuwar wani sabon guguwar hare-hare, amma babbar tambaya anan. Shin wannan fahimtar juna za ta iya zama farkon kawo karshen rikicin tsakanin Amurka da Iran, ko kuwa wani dakatarwa ne na wucin gadi a cikin rikicin da ba a warware muhimman batutuwansa ba?
Your Comment