11 Yuni 2026 - 16:26
Source: ABNA24
Afrika: Yadda Mulkin Mallaka Ya Mayar Da Musulman Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya Bare

Wani sabon bincike na jami'a ya nuna cewa tashe-tashen hankula da ake yi wa Musulmai a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ba iya sakamakon yaƙin cikin gida na 'yan shekarun baya ba ne kawai, sai dai, sun samo asali ne daga tsarin mulkin mallaka mai dogon zngo da zurfi da aka shiryawa kasar, ta hanyar samuwar gwamnatin zamani da sake fasalin asalin ƙasa.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya habarta cewa: Wata makala ta ilimi da aka buga a cikin wata jarida mai daraja ta "Jaridar Nazarin Afirka" da ke da alaƙa da Jami'ar Cambridge, yayin da take nazarin tashe-tashen hankula a kan Musulmai a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, ta jaddada cewa ba za a iya taƙaita rikicin da ƙasar ke ciki a yanzu ga rikice-rikicen soji da yaƙin cikin gida kawai ba, sai dai dole ne a nemo tushensa a cikin tarihin mulkin mallaka da tsarin samuwar asalin ƙasa.

Bisa ga wannan bincike, Musulmai a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a cikin shekaru masu tsawo sannu a hankali sun shiga cikin wani yanayi inda ba a bayyana su a matsayin wani ɓangare na ƙasa daidai gwargwado yadda ya kamata ba, sai dai an bayyana su a matsayin ƙungiyar da ba ta dace ba kuma ba ta cikin yanki na jikin babbar al'ummar kasar.

Afrika: Yadda Mulkin Mallaka Ya Mayar Da Musulman Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya Bare

Gadon Mulkin Mallaka da Farkon Rarrabuwar Asali

Wannan bincike ya nuna cewa a lokacin mulkin mallaka na Faransa, tsarin siyasa da gudanarwa an tsara su ne ta yadda ba a sami cikakken haɗin kan al'ummomin Musulmai a cikin tsarin mulkin mallaka ba.

Sakamakon haka, Musulmai na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun kasance a gefen tsarin tattalin arziki da zamantakewa, kuma wannan yanayin a hankali ya haifar da rarrabuwar asalin yan kasanci mai dorewa.

A cewar marubuci, wannan rarrabuwar ta tarihi ta sa Musulmai na wannan ƙasa a cikin tunanin siyasa da zamantakewa a matsayin wata ƙungiya ta daban kuma ba ta cikin asalin yan ƙasa.

Afrika: Yadda Mulkin Mallaka Ya Mayar Da Musulman Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya Bare

Bayan 'Yancin Kai; Ci Gaba Da Zama A Gefen

Bayan samun 'yancin kai na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, ana sa ran waɗannan rarrabuwa za su ragu, amma bincike ya nuna cewa gwamnatocin bayan 'yancin kai a lokuta da yawa sun sake maimaita irin waɗannan tsare-tsare na baya.

A cikin jawabin kishin ƙasa na hukuma a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, an samar da hoton ɗan ƙasa na gaske wanda a cikinsa, Musulmai na wannan ƙasa sau da yawa ba a haɗa su gaba ɗaya acikin tsarin ba, kuma a wasu lokuta ana nuna su a matsayin baƙi ko yan gudun hijira. Ko da sun rayu tsawon tsatso a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Afrika: Yadda Mulkin Mallaka Ya Mayar Da Musulman Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya Bare

Yaƙin Cikin Gida Da Yaduwar Tashe-Tashen Hankula

Waɗannan rarrabuwar ta tarihi a shekara ta 2013 miladiyya, tare da fara yaƙin cikin gida a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, sun bayyana a matsayin tashin hankali a fili.

A wannan lokacin, ƙawancen 'yan tawayen da ake kira "Seleka" sun karɓi mulki a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, kuma a matsayin martani ga hakan, ƙungiyoyin mayaka na Kirista da aka sani da "Anti-Balaka" suka bulla.

Rikici tsakanin waɗannan ɓangarorin biyu cikin sauri ya sami yanayin addini da kabilanci, kuma sakamakonsa shi ne kisan kiyashi ga fararen hula Musulmai, lalata masallatai da unguwannin Musulmai, da kuma korar dubban daruruwan mutane a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

A yankuna da yawa na biranen Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, al'ummomin Musulmai an tilasta musu barin gidajensu gaba ɗaya, kuma yanayin al'umma na wasu garuruwa ya canza gaba ɗaya.

Afrika: Yadda Mulkin Mallaka Ya Mayar Da Musulman Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya Bare

Musulmai A Matsayin Waɗansu Bare

Sakamako mafi mahimmanci na wannan bincike shi ne cewa tashe-tashen hankula a kan Musulmai a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya bai takaita ga samfurin yaƙi ba ne kawai, a'a, sakamakon dogon tsari ne na mayar da su waɗansu bare.

A cikin wannan tsari, Musulmai na wannan ƙasa a hankali a cikin labarin hukuma na al'umma an nuna su a matsayin waɗanda ba 'yan ƙasa ba, wani abu da ya zo daga wajen kasa ko barazana ga asalin ƙasa. Wannan dubin tarihi ya sa a lokutan rikici, tashe-tashen hankula a kansu su sami halaccin zamantakewa cikin sauri.

Afrika: Yadda Mulkin Mallaka Ya Mayar Da Musulman Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya Bare

Rawar Tsarin Siyasa Da Raunin Gwamnati

Wannan makala ta kuma jaddada cewa raunin cibiyoyin gwamnati, gasar ƙungiyoyin da ke ɗauke da makamai da yin amfani da asalin addini don siyasa, sun taka muhimmiyar rawa wajen tsananta rikici a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

A cikin irin wannan yanayi, tashin hankali ba wani lamari ne na lokaci-lokaci ba, a'a, ya zama wani ɓangare na tsarin siyasa da zamantakewa na wannan ƙasa kamar sauran kasashen Afirka da ‘yan mulkin mallaka suka lalata suka saka ma’aikatansu.

Afrika: Yadda Mulkin Mallaka Ya Mayar Da Musulman Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya Bare

Takaitaccen Bincike

A takaitaccen bayanin wannan makala tayi binceke ne, don fahimtar rikicin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, dole ne tsalle nazarin tsaro a mai da hankali ga tushen tarihi da zamantakewa.

A ra'ayin marubuci, Musulmai na wannan ƙasa a cikin dogon tsari na tarihi an mayar da su waɗansu bare. Tsarin da sakamakonsa a yau yana ci gaba da kasancewa a matsayin tashin hankali, kora da wariya a tsarin siyasa da zamantakewa da asalin kasar.

Wannan bincike ya nuna cewa rikicin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ba wai kawai yaƙin cikin gida ba ne, a'a, sakamakon tsari ne na tarihi wanda asalin ƙasa ya samo asali a kan watsi da kawar da wani ɓangare na al'umma. Tsarin da sakamakonsa har yanzu yana ci gaba da kasancewa ta hanyar tashe-tashen hankula a kan Musulmai.

..............

Your Comment

You are replying to: .
captcha