10 Yuni 2026 - 22:47
Source: ABNA24
Ranar Mubahala Ranar Tabbatar Da Gaskiyar Sakon Manzon Rahama (As) Ga Dukkan Halittu

Ranar 24 Zulhijjah a irin wannan rana ne a shekarata 9 bayan Hijira waki’ar Mubahala ta auku dake Nunan Gaskiya tare da tabbatar Annabcin Manzon Allah SAWa da Matsayi Na Iyana Gidan Annabi Sawa.

Kamar yadda malaman tarihi sukan kawo riwayoyi da dama a littafansa da suke dauke da faruwar wannan lamari na Mubahala wato neman tsinuwar Allah domin tabbatar da gaskiyar wani abu tsakanin mutane guda biyu don bayyana wanda yake da gaskiya kamar yadda ya faru tsakanin Annabi Muhammad SAWA da Kirisotocin Najran bayan tattaunawa mai tsawo da tambayoyi da sukayi Annabi SAWA akan abubuwa da dama wanda har Allah Taala ya saukar da Ayiyo dangane da bayyana hakikanin abunda sukai tanbaya akai amma basu yarda ba akarshe dai aka sanya rana domin gudanar da wannan tsinuwa wanda bayan zuwan ranar Kiristocin saboda abinda suka gani na zuwan Annabi da Iyalansa SAWA sunki yarda da ayi wannan tsineneniya.

Kamar yadda yan Shi’ah suke da Iitikadin cewa wannan lamari bama yayi nuni ne kadai wajen tabbatar da gaskiyar Annabcin Annabi ba a’ah yayi nuni har wala yau da Falala da girma da matsayi na wadanda suke tare dashi Imam Ali Sayyidah Fatimah Imam Hasan Da Imam Husain AS.

Kamar yadda ayar take nuni da cewa mu zo da yayanmu da Matanmu da Kawunan mu to anan kamar yarda Shi’a suka tafi akai manzon Allah da Imam Ali sune Kawunan mu sayyida Fatima kuma Itace Matayan mu Imam Hasan da Husain sune Yayayan mu.

Kaga kenan Imam Ali yana a matsayin Manzon Allah SAWA kamar yarda yazo A hadisai da dama duk shi ba Manzo bane wasiyyin Manzon Ne SAWA,

Kamar yadda ta 61 cikin suratu Ali Imran tayi Nuni da hakan.

Your Comment

You are replying to: .
captcha