29 Mayu 2026 - 23:34
Source: ABNA24
Adadin Wadanda Suka Shahada A Hare-Haren Da Isra'ila Ta Kai A Lebanon Ya Kai 3,324

Adadin wadanda su kai shahada a hare-haren da sojojin mamaya na Isra'ila suka kai wa Lebanon tun daga ranar 2 ga Maris, duk da yarjejeniyar tsagaita wuta, ya karu da 55, inda ya kai 3,324.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya habarta cewa: Sojojin mamaya na Isra'ila na ci gaba da kai hare-hare a Lebanon, duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da ta fara aiki daga ranar 17 ga Afrilu, wacce kuma aka tsawaita da kwanaki 45 daga ranar 17 ga Mayu.

Ma'aikatar Lafiya ta Lebanon ta fitar da sabbin bayanai game da adadin wadanda su kai shahada da wadanda suka jikkata sakamakon hare-haren da Isra'ila ta kai tun daga ranar 2 ga Maris.

Bisa ga bayanan, adadin wadanda suka shahada a hare-haren sojojin Isra’ila ya karu da 55 a cikin sa'o'i 24 da suka gabata, inda ya kai 3,324, yayin da a wannan lokacin mutane 10,027 suka jikkata.

…………………………………..

Your Comment

You are replying to: .
captcha