26 Mayu 2026 - 11:39
Source: ABNA24
Fassarar Saƙon Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci (Dm) Dangane Da Taron Hajjin Bana

"Labbayk, Allahumma labbayk. Labbayk, la sharika laka labbayk. Innal hamda wan ni'mata laka wal mulk... Ya Allah! Na karɓi kiranka; babu abokin tarayya a gare Ka, kuma dukkan yabo, ni'ima, da mulki daga gareka ne kuma mallakinka ne...".

Bismillahir Rahmanir Rahim

"Labbayk, Allahumma labbayk. Labbayk, la sharika laka labbayk. Innal hamda wan ni'mata laka wal mulk... Ya Allah! Na karɓi kiranka; babu abokin tarayya a gare Ka, kuma dukkan yabo, ni'ima, da mulki daga gareka ne kuma mallakinka ne...".

Lokacin Hajjin bana ya sake zagayowa, kuma al'ummar Musulmi sun ɗaura tufafin ihramin ibada suna masu yin talbiya –amsa kira- domin yin hijira daga rayuwar duniya ta al'ada zuwa rayuwar Allah ta jindadi; rayuwar tauhidi bisa bautar Ubangiji, da kuma korewa da kuɓuta daga abin da ba Allah ba.

Amma damar wannan hijira ba ta takaita ga mahajjata da masu ziyarar Baitullah na bana kaɗai ba; duk 'yan'uwa musulmi maza da mata na Iran da ma dukan duniya, waɗanda suka yi Hajji a shekarun baya da suka shige, sharadin wannan hijira shi ne ɗaura rigar ibada ta dindindin a kan ambaton Allah; dawafi na dindindin a kan gaskiya; tafiyar dindindin a tsakanin manyan duwatsu masu hatsari na ayyukan Allah; jifar dindindin ga shaidan da 'yan tawagansa duka da abubuwan ruɗinsa; tsayuwa mai hade da kulawa da addu'a da tawali'u; ciyar da talakawa da matafiyi; yanka son zuciya da sha'awa masu ɗaurewa, da kawar da ƙazantuttukan ciki; a kuma kowane hali, kasancewa a shirye don hidima da ɗaga tutar kare gaskiya.

Kuma hakanan al'ummar Iran ta kasance a lokacin "Miqatin Juyin Juya Halin Musulunci, - kafuwar juyin juya halinsu musulunci- ta shiga hanyar wannan hijira. Ta karɓi kiran Ibrahim na Babban Khumaini, ta tuɓe rigar karɓar mamaya, ta sa rigar jindadin duniya da lahira, tana yin talbiya cikin sassarfa tana ƙoƙari don ta yi dawafi a kan ingantaccen taskar Musuluncin Muhammadu (SAW) da kuma kusantar da kanta ga hasken adalci na duniya da Wilayatul Uzma…

... Kuma da wannan makamin na "Allahu Akbar" ne al'ummar Iran ta yi yunkuri a cikin shekaru arba'in da bakwai da suka wuce, ta hambarar da tsarin mulkin kama-karya mai dogaro da kasashen waje na Pahlavi, ta yanke hannu da ƙafar Amurka mai kwadayi da girman kai daga ƙasar, kuma gaba ɗaya ta yanke tasirin Sahayoniyya. Da wannan makamin na "Allahu Akbar" ne bayan mamayar da tsarin mulkin Ba'ath na Saddam ya yi wa ƙasar Iran, mayaƙa masu kishi da samari masu sadaukar da kai suka rubuta yakin gwarzancin shekaru takwas na tsaro mai albarka, kuma duk da goyon bayan dukkan manyan ƙasashen Gabas da Yamma ga tsarin Ba'ath, suka durƙusar da shi, kuma suka ci gaba da wannan tsayin daka har tsawon shekaru masu zuwa a wajen fuskantar killacewar tattalin arziki, juyin mulki, takunkumi na zalunci, hare-haren siyasa, farfaganda da tattalin arziki na abokan gaba a kan Jamhuriyar Musulunci, da ƙarfi da tsayin daka.

Wannan makamin "Allahu Akbar" ne ya ƙarfafa alakar da ke tsakanin al'ummar Musulunci da matasa mayaƙan gwagwarmaya daga Iran zuwa Lebanon da Falasdinu da Iraqi da Sham, daga Afirka da Yaman zuwa Afghanistan da Pakistan da dukkan al'ummomi masu 'yanci na duniya, har wannan igiya mai ƙarfi ta tashi don kare rayuwar al'ummar Musulunci a gaban masu keta iyaka da ma'abota mamayar Sahayoniyya, ta murƙushe Da'ish, ta haifar da Tufanu Al-Aqsa, kuma ta sa ran gwamnatin Sahayoniyya mai rauni ya girgiza….

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha