Kamfanin dillancin labarai na Ahlul Bait (AS) - ABNA - ya ruwaito cewa: A fagen siyasa, Benyamin Netanyahu a wani faifan bidiyo da kafafen yada labarai na Ibraniyawa suka fitar, ya bayyana cewa ya umurci sojojin Gwamnatin Isra’ila da su kara saurin ayyukan soji kuma su ci gaba da kai hare-hare da karfi, domin a cewarsa, dole ne su murkushe Hizbullah.
Netanyahu a lokaci guda ya tabbatar da kalubalen da jiragen marasa matuki na Hizbullah ke haifarwa, ya ce: "Gaskiya ne suna amfani da jirage marasa matuki masu dauke da fasahar fiber optics a kanmu, amma muna da tawaga ta musamman domin fuskantar wannan batu, kuma za mu warware wannan matsalar".
Ya kuma bayyana cewa, ya cimma yarjejeniya da Donald Trump shugaban Amurka, game da kare hakkin Isra'ila na fuskantar barazana a kowane fage.
"Betzalel Smotrich" ministan kudin Sahayoniyya shi ma ya sanar da ware wani kasafi na musamman wanda darajarsa ta kai shekel biliyan biyu (kimanin dala miliyan 692) domin bunkasa na'urorin fuskantar jirage marasa matuki.
Ya ce a cikin wata sanarwa mai tayar da hankali: "A kan kowane jirgi mara matuki mai fashewa, ya kamata gine-gine 10 a Beirut su ruguje".
Haka kuma "Itamar Ben-Gvir" ministan harkokin tsaron cikin gidan Sahayoniyya, ya bukaci a katse wutar lantarki a Lebanon, a mamaye kogin Zahrani, da fadada yakin a fagage da dama.
A halin da ake ciki, ma’aikatar rediyo da talabijin ta Sahayoniyya ta ruwaito cewa, "Eyal Zamir" shugaban hafsoshin soji na wannan gwamnati tare da kwamandan yankin arewa, sun gabatar da sabbin tsare-tsare na ayyuka don fadada hare-hare a Lebanon da canza ma'auni a gaban Hizbullah ga jami'an siyasar Sahayoniyya. Ana shirin duba wadannan tsare-tsare a babban taron tsaro.
Tsagaita Wuta Mai Rauni Da Tattaunawar Da Ake Gabatarwa
Wadannan abubuwan da suka faru na zubar da jini suna faruwa ne a daidai lokacin da aka samu tsagaita wuta tsakankanin Amurka da tsakanin bangarorin, kuma Lebanon da gwamnatin Isra’ila suna shirye-shiryen gudanar da zagaye na hudu na tattaunawar kai tsaye a ranakun 2 da 3 ga watan Yuni.
Kafin wannan kuma, ana shirin gudanar da taron tawagogin soji na bangarorin biyu a karshen watan Mayu.
Dangane da haka, Joseph Aoun ya nanata cewa ficewar gwamnatin Isra’ila gaba daya daga kudancin Lebanon wani buri ne na kasa wanda ba za a yi sulhu a kai ba, ya ce: "Tattaunawa ba yana nufin mika wuya ba, a'a, tabbatarwa ce ga ikon Lebanon da kuma keɓance makamai a hannun sojoji da cibiyoyin doka na kasar".
A gefe guda kuma, Sayyid Abbas Araghchi ministan harkokin waje na jamhuriyar Musulunci ta Iran, a cikin sakonni daban-daban zuwa ga Nabih Berri da Naim Qasim, ya nanata ci gaba da goyon bayan Iran ga 'yancin kai, ikon mallaka, da cikakken yankin Lebanon, da kuma gwagwarmayar kasar a kan mamayar gwamnatin Isra’ila.
Kididdigar Wadanda Suka Rasa Rayukansu
Dangane da kididdigar hukuma ta ma'aikatar lafiya ta Lebanon, tun lokacin da aka fara fadada ayyukan gwamnatin Isra’ila a Lebanon a ranar 2 ga Maris da ta wuce, adadin wadanda sukai shahada daga Lebanon ya kai 3,185, yayin da aka samu raunatar 9,633.
Haka kuma, fiye da 'yan kasa miliyan daya na Lebanon sun zama 'yan gudun hijira daga gidajensu sakamakon fadace-fadace da hare-haren sojojin gwamnatin Isra’ila.
Your Comment