14 Mayu 2026 - 23:47
Source: ABNA24
Shin Jirage Marasa Matuƙa Na Fiber Optic na Hizbullah Za Su Canza Ma'aunin Yaƙi A Kudancin Lebanon?

Wani kwararren masanin harkokin soji ya yi imanin cewa jirage marasa matuka na kunar bakin wake na Hizbullah sun zama barazana fiye da makami yaƙi mai inganci.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: jirage marasa matuka na kunar bakin wake na Hizbullah, waɗanda ake sarrafa su da fasahar fiber optic, ba wai kawai sun zama abin damuwa ga Isra'ila wajen wahalar gano su ta radar da kuma ikon kai harinsu kaitsaye ba ne har ma sun zama makami mai mahimmanci (strategic weapon) wanda zai iya tilasta wa Tel Aviv sake duba shirinta na kafa yankin da ba za a kai hari ba a kudancin Lebanon.

Dangane da rahoton gidan talabijin na Al Jazeera, a cewar "Hassan Jouni", Birgediya Janar mai ritaya kuma masanin harkokin soji, waɗannan jirage marasa matuka sun zama ƙalubale na dabarar yaƙi har zuwa gibin soji ga sahayoniyawa, saboda sun fallasa wani babban rauni a cikin tsarin tsaron wannan gwamnatin.

Jouni a cikin wani bincike ga Al Jazeera ya nanata cewa Sahayoniya a cikin 'yan makonnin da suka gabata ta yi ƙoƙari ta hanyoyi daban-daban ta dakatar da waɗannan jirage, amma ba ta yi nasara ba a wannan fanni. Lamarin da ya mayar da amfani da waɗannan jirage daga wani aiki na wucin gadi zuwa wani ɓangare na sabon tsarin yaƙi na Hizbullah.

Shin Jirage Marasa Matuƙa Na Fiber Optic na Hizbullah Za Su Canza Ma'aunin Yaƙi A Kudancin Lebanon?

Yayin da barazanar waɗannan jirage ke ƙaruwa, sojojin sahayoniya da farko sun yi ƙoƙarin harbo su kafin su kai ga inda aka harba su, amma sun kasa yin hakan. Daga baya suka yi ƙoƙarin kai hari ga wuraren da ake harbi su; wani aiki da aka yi ta hanyar kutsawar kasa a yankuna kamar Wadi al-Raj da kewayen Zutar ta Gabas da sauran yankunan da ke da yanayin ƙasa mai sarkakiya.

Duk da haka, a cewar Jouni, aikin ƙasa ma bai iya rage barazanar waɗannan jirage ba; saboda mai sarrafa su na iya ɓoyewa a cikin bishiyoyi. Bugu da ƙari, gano kebul ɗin fiber optic mai tsananin sirarantaka da ke haɗa jirgin da mai sarrafa shi abu ne mai wuyar gaske.

Shin Jirage Marasa Matuƙa Na Fiber Optic na Hizbullah Za Su Canza Ma'aunin Yaƙi A Kudancin Lebanon?

Sahayoniyoyi kuma sun yi ƙoƙarin fuskantar waɗannan jirage da taruna da makamai masu fashewa kafin su kai ga inda aka nufa, amma wannan hanyar ma ta kasa saboda babu wani zafi da radar za ta iya ganowa. A ganin wannan masanin harkokin soji, wannan lamari ne ya sa waɗannan jirage marasa tsada suka zama makami mai mahimmanci a wannan yaƙin.

Makami Mai Mahimmanci

A cewar Jouni, waɗannan jirage suna iya tilasta wa Isra'ila ta sake duba shirinta na killace yankin da ba za a kai hari ba a kudancin Lebanon; saboda a inuwar wannan barazana mai ci gaba, ba zai yiwu a zauna a irin wannan yanki ba.

Ya kara da cewa yaƙe-yaƙe koyaushe suna tare da abubuwan mamaki. Waɗannan jirage su ne babban abin mamaki na wannan yaƙin, saboda suna iya hana Isra'ila tsare tare kafa kanta a yankin da ba za a kai hari ba.

Don ƙarin bayani, ya ce: Wannan lamari ba sabon abu ba ne a yaƙe-yaƙe; kamar yadda sojojin Masar a da suka yi nasarar karya katangar Barlev mai ƙarfi ta amfani da famfunan ruwa, saboda sun sami hanyar yin amfani da wani sabon tunani.

Ya zuwa yanzu Hizbullah ta yi amfani da waɗannan jirage wajen kai hari ga yankuna daban-daban kamar: Asba'ul Galili, Safad, da sauran garuruwan da sahayoniyoyi ke zama kusa da iyaka. Amma a yau Alhamis ta yi wani aiki na daban, inda ta yi amfani da ɗaya daga cikin waɗannan jirage ta kai hari a yankin Ras al-Naqoura a arewacin yankunan da aka mamaye, wanda ya yi sanadiyar raunata sojoji 17.

Hizbullah kuma tana amfani da waɗannan jirage wajen kai hari ga sojoji da kayan aikinsu da ke a ƙauyukan Lebanon, ƙauyuka kamar Al-Bayyadah da Houla, waɗanda aka tilasta wa mazaunansu yin hijira. Kamar yadda jaridar Yedioth Ahronoth ta rubuta, wannan lamari ya sa sojojin sahayoniya ke jin fargabar kasancewa a waɗannan yankuna.

A gefe guda, Isra'ila a yau ta tsananta hare-harenta a kudancin Lebanon, ta kuma gudanar da ayyukan fashewa a kewayen kogin Litani har zuwa yankunan da ke kusa da kogin Zahrani da yankin Beqaa ta Yamma.

..................

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha