13 Mayu 2026 - 10:25
Source: ABNA24
Iran: An Rataye Ɗan Leƙen Asirin Mossad

Ehsan Afrashteh, ɗan leƙen asirin da Mossad ta horar a Nepal an kama shi da tuhumar sayar wa da Isra'ila bayanan sirrin ƙasar Iran, wanda bayan bincike na sharia an zartar masa da hukuncin kisa

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: An zartar da hukuncin kisa ga Ehsan Afrashteh, ɗan Mustafa, wanda aka kama tare da gurfanar da shi a gaban kotu bisa zargin leƙen asiri da ba da haɗin kai na bayanan sirri ga Sahayoniya. 

Bayan kammala dukkan matakan shari'ar laifuka da kuma amincewa da hukuncin daga Kotun Koli ta ƙasar, da safiyar yau an zartar da hukuncin da ya dace da ayyukansa, inda aka rataye shi.

Tun daga farkon tuntuɓarsa da jami'in Mossad na farko, wanda ake magana ya yi tuntuɓar a matakai da yawa ta hanyar kafafen sadarwa da saƙonni, daga baya kuma ya ci gaba da tuntuɓar su ta hanyar imel.

Da farko, ya kasance yana aiwatar da umarnin jami'an Mossad a ƙarƙashin sunan direban tasi na intanet.

Afrashteh a tsawon haɗin gwiwarsa da sahayoniya, ya ƙware a harsunan Ingilishi, Faransanci da Ibrananci, kuma sunan da aka ba shi a cikin ƙungiyar Mossad shi ne "James".

Wanda aka yanke masa hukunci, a tsawon haɗin gwiwarsa da Mossad, yana aika wa jami'an leƙen asirin Mossad aƙalla sakon imel 4 zuwa 5 a kowane wata, baya ga tuntuɓar murya da sauransu. An yi musayar saƙonni sama da 300 a tsakaninsu.

...................

Your Comment

You are replying to: .
captcha