Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Jaridar New York Times a wani rahoto mai girgiza rai ta yi tsokaci game da cin zarafi da keta haddi sojojin Isra'ila ke yi wa fursunonin Falasdinu a gidajen yarin Isra'ila.
Nicholas Kristof, marubuci mai bincike na New York Times, a wani sabon rahoto ya tona asirin yadda ake yi wa fursunonin Falasdinu da yawa fyade da cin zarafinsu a gidajen yarin Isra'ila. Ya kuma bayyana cewa da yawa daga cikin wadanda abin ya shafa, duk da tsoratarwa da yi musu barazana, sun yarda su ba da shaida kan abin da ya same su.
Kristof a cikin wannan rahoton ya rubuta cewa wasu fursunonin Falasdinu sun ce an yi musu barazana da kisa ko fyade daga sojojin Isra'ila idan sun yi hira ko tona asirin bayanai, amma duk da haka sun yanke shawarar kada su yi shiru.
Dangane da wannan rahoton, wani fursuna ɗan Falasdinu ya rawaito cewa a rana guda, an yi masa fyade sau uku a gidan yarin Isra'ila, kuma na uku ya faru ne bayan ya yi ƙoƙarin nuna kin amincewarsa. Wata budurwa 'yar Falasdinu kuma ta ce masu gadin suna shiga cikin dakin da take a farkon kowane lokacin aiki, suna tilasta mata ta tuɓe, sannan su ci zarafinta.
Your Comment