Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Sheikh Na'im Qasim, Babban Sakataren Hizbullah Lebanon, a cikin wani sako da ya aika zuwa ga kwamandoji da mayaƙan gwagwarmaya, ya jaddada: "Ba za mu taɓa barin fagen daga ba, domin farshin gwagwarmaya ƙasa ya ke da farshin mika wuya".
A cewar rahoton tashar Al-Manar, ainihin sakon Sheikh Na'im Qasim zuwa ga kwamandoji da mayaƙan da ke fagen daga yazo kamar haka:
"Jiragenku marasa matuki suna sauka kan ƙasa suna masu shake masu mamaya na Sahayoniyawa. Waɗannan jiragen na ku marasa matuki suna tsoratar da miyagu da azzaluman doron ƙasa. Ba za ku mutu ba; ko dai ku wanzu a fagen daga ko kuma ku zama shahidai, kuma kuna masu rayuwa kusa da Ubangijinku masu azurtuwa.
Sun ce taku ta ƙare kuma za ku sha kaye! Amma jihadin ku ya haifar da gagarumin juriya wanda ya ba duniya mamaki. Kun zaɓi rayuwa mai daraja ba wulaƙanci ba. Ku ne alamar 'yanci ba mika wuya ba, jagoranci ba bauta ba, 'yancin kai ba bautar wani ba. Ku 'ya'ya ne masu daraja ga shugaban shahidai na al'umma, Sayyid Hassan Nasrallah, Sayyid Hashim, da sauran shahidai, waɗanda suka jikkata, da fursunoni.
Muna fuskantar maƙiyi Sahayoniya mai laifin ta’addanci da zalunci, wanda ke samun goyon baya daga manyan azzaluman Amurka da wasu ƙasashe masu bin sawun su. Ƙaramin rukuni ne da ƙarancin kayan aiki ke fuskantar wannan maƙiyi, amma wannan rukuni Allah Maɗaukaki ne ke taimakonsa, don haka za mu yi nasara. Muna shaida cin zarafin Amurka da Sahayoniyawa da nufin su durƙusar da Lebanon su mayar da ita wani ɓangare na shirin 'Babbar Isra'ila'.
Duk tsawon lokacin da zai ɗauka da sadaukarwar da ake buƙata, ba za mu taɓa mika wuya ba, kuma za mu ci gaba da kare Lebanon da al'ummarmu; domin farshin gwagwarmaya ƙasa kadan ne akan farshin mika wuya. Ba za mu taɓa barin fagen daga ba, kuma za mu mayar da shi jahannama ga Isra'ila. Ba za mu taɓa komawa ga yanayin da muke ciki kafin ranar 2 ga Maris ba, kuma za mu mayar da martani ga cin zarafin maƙiyi.
Yarjejeniyar Iran da Amurka wadda ta haɗa da dakatar da cin zarafi a kan Lebanon, ita ce kati mafi ƙarfi don dakatar da cin zarafi. Muna godiya ga Iran saboda kulawarta ga Lebanon da al'ummarta, kuma muna godiya ga duk wani bangare da ya taka rawa wajen dakatar da cin zarafi a kan Lebanon. Alhakin tattaunawa don cimma burin Lebanon alhakin gwamnati ne. A shirye muke mu ba da hadin kai ga gwamnati tare da dakatar da cin zarafin maƙiyi Sahayoniya a cikin teku, ƙasa, da sama, da kuma 'yantar da yankunan da aka mamaye, da kuma girke sojoji. A shirye muke mu ba da hadin kai don 'yantar da fursunoni, dawo da mutane gidajensu, da sake gina abinda aka rusa.
Muna son ja da baya daga tattaunawar kai tsaye wacce kawai amfanin Isra'ila take dauke da shi da kuma rashin bayar da wani fifiko na zahiri daga Beirut. Batun makamai da gwagwarmaya da al'amuran cikin gida na Lebanon ba su da wata alaka da mutanen wajen kasar.
Bayan cimma burika biyar, Lebanon za ta sake nazarin yanayin dabarun da suka shafi tsaron cikin gida ta hanyar amfani da abubuwan da ke da ƙarfi da ta mallaka ciki har da gwagwarmaya. Ina kiran a gudanar da cikakken bincike na siyasa da tsaro a matsayin wani ɓangare na dabarun tsaron kasa a matakan siyasa, tattalin arziki, da soja.
Dukkan gwagwarmayarmu tana da nufin dakatar da cin zarafi ne, kuma ba za mu taɓa barin fagen daga ba".
………………………………………
Your Comment