Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: A kimantawar has ashen da akai Iran har yanzu tana da kusan kashi 70% na na'urorin harba makamai masu motsi da ta shimfida a duk faɗin ƙasar, kuma ta kiyaye kusan kashi 70% na tarin makamanta da take da su kafin yaƙin. Iran ta sami damar shiga kusan kashi 90% na wuraren ajiya na ƙarƙashin ƙasa da na harba makamai masu linzami a duk faɗin ƙasar.
Wani ɗan jarida Ba'amurke ya kara da cewa: "Biranen Makamai masu linzami" na Iran an binne su a zurfin mita 500 a cikin wani dutse na granite. Wanda Amurka ba ta mallakin makamin da zata iya rusa shi ba domin makamin da sojojin Amurka ke amfani da shi don rushe sansanonin da ke ƙarƙashin ƙasa, yana iya shiga cikin kasa ne iya mita 60 kawai. Iran tana riƙe da katin nasara a hannunta.
…………………………………..
Your Comment