11 Mayu 2026 - 23:16
Source: ABNA24
Isra’ila: Mun Koma Yanayin Bugi In Buga Tsakaninmu Da Hizbullah A Martani

Bisa ga daidaiton Hizbullah, idan gwamnatin Isra’ila ta kai hari ga yankin Dahiya, Hizbullah za ta kai hari ga Haifa; idan ta kai hari ga Beirut, za su kai hari ga Tel Aviv; kuma idan Sahayoniya suka kai hari ga kudancin Lebanon, za su kai hari ga ƙauyukan Sahayoniyawa da ke arewacin yankunan da aka mamaye.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Yanzu kenan tashar ta 12 ta gwamnatin Sahayoniya ta ce wani jami'in sojan Sahayoniya ya tabbatar da cewa "wannan gwamnati ta koma yanayin daidaiton martani da Hizbullah kena kwabo da kwabo.

Tashar 12 ta gwamnatin Sahayoniya ta tabbatar da cewa: Gano jiragen marasa matuki na fiber optic na Hizbullah yana da wuya ƙwarai. Gano su ko bibiyar waɗannan ƙananan jiragen da wuri abu ne mai matukar wahala, kuma hakan ya sanya kakkabo ya zama mai sarkakiya matuka. Barazanar jiragen marasa matuki masu kai harin kunar bakin wake sun yi tasiri sosai kan ayyukan "sojojin" Isra'ila a cikin ƙasar Lebanon.

Hizbullah ta Lebanon ta sanar da cewa ta kai hari da jirgi mara matuki kan sabbin wuraren harba manyan bindigogi na sojojin Isra'ila da aka kafa a garin al-Adaisah da ke kudancin Lebanon.

Hizbullah ta yi amfani da lokacin tsagaita wuta don haɓaka jiragen marasa matuki masu kai harin kunar bakin wake; wani makami da har yanzu ba mu san yadda za mu iya fuskantar su ba yadda ya kamata. Yanayin ayyukan sojojin Isra'ila ya canja ƙwarai da gaske saboda barazanar jiragen marasa matuki masu kai harin kunar bakin wake.

……………………………………..

Your Comment

You are replying to: .
captcha