25 Afirilu 2026 - 00:20
Source: ABNA24
Iran Ta Tarwatsa Cibiyar Leƙen Asirin Kafin Aikewa Da Bayanan Sirri

Sojojin Imam Zaman (amincin Allah ya tabbata a gare shi) reshen cikin cibiyar Leken Asiri ta IRGC sun sami nasarar gano da kuma wargaza wata kafar leken asiri da ke da alaƙa da Mossad (hukumar leken Asiri ta gwamnatin Sahyoniya) a cikin jerin ayyukan da ta tsara ta gudanar.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Jami'an tsaron Iran sun lalata wata cibiyar leken asiri kafin ta aike bayanai kan wuraren da na'urorin tsarin tsaro suke.

An kama membobin wannan kafar tare da taimakon rahotannin jama'a. Cibiyar Leken Asiri ta IRGC ta nemi jama'a da su bayar da rahoton duk wani lamari da ake zargi ga number waya 114 ko adireshin yanar gizo na @jasosyab da ke kan kafar sadarwa ta Rubika da Eta.

Your Comment

You are replying to: .
captcha