24 Afirilu 2026 - 22:17
Source: ABNA24
Iran Ta Kwace Wasu Jiragen Ruwan Amurka + Bidiyo

An fitar da bidiyon farko na kama jiragen ruwan Amurka a mashigar Hormuz da mayakan ruwa na IRGC su ka yi. 

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Iran ta kai jiragen da ta kwace zuwa Bandar Abbas. Jiragen ruwa guda 2 da Iran ta kwace a ranar Laraba an kai su Bandar Abbas. Jirgin na farko ya kasance yana dauke da rukunin jigilar kayayyaki na Bahar Rum, MSC, wanda shine kamfani mafi girma na jigilar kaya a duniya. Jirgin yana tafiya ne a ƙarƙashin tutar Panama. Wani dan uwan ma'aikatan jirgin ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa: "Kimanin Iraniyawa 20 ne suka shiga jirgin, dauke da makamai a halin yanzu, ma'aikatan jirgin suna karkashin ikon Iraniyawa, amma sojojin Iran suna kyautata musu mu'amala. Jirgi na biyu kuma shine EPAMINONDA, Kamfanin Takmar Shopping na Girka ne ke tafiyar da shi kuma ya ɗaga tutar Laberiya kuma yana da ma'aikatan jirgin 21 daga Ukraine da Philippines. 

An kai wa jirgin hari a nisan mil 20 daga arewa maso yammacin Oman kai tsaye da roka na RPG da wani jirgin ruwan sintiri na IRGC.

Your Comment

You are replying to: .
captcha