Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Ofishin Hulda da jama'a na Rundunar Sojan Juyin Juyin Juya Halin Musulunci: A safiyar yau, sun kai hari kan sassan cibiyoyin masana'antu da wuraren sojoji da hedkwatar kwamandoji da sassan sojojin Sahayoniyya a yankin Kudu, tsakiyar Tel Aviv da arewacin yankunan da aka mamaye.
Tare kiran ramzin (Ya Ummal Baneen) sadaukarwa ga duk uwayen shahidai, musamman Ezzat Banu (mahaifiyar shahidin da ya yi shahada) a wannan hare-haren an yi anfani da makamai masu linzami da nau'ukan manyan makamai masu linzami na Khorramshahr, Khyber Shikan da Emad da ke ɗauke da manyan kawunan yaƙi da ake iya sarrafawa da nau'ukan jiragen yaƙi marasa matuka masu tarwatsa komai suka tunkara. Wanda ko wane ɗaya daga cikisu ya kai ga inda aka harba shi tare da haifar barna yawa.
Wuraren da aka hara sun haɗa da: wasu wurare a cikin Dimona da Naqb da Beer Asba da Ramat Gun, a ci gaba da gudanar da salon yaƙi na wuta ga wuta wuraren sun fuskanci munanan hare-hare bayan gazawar na'urorin tsaron saman Isra'ila masu ci gaba. Babban nasara ga Sojojin jamhuriyar Musulunci ta Iran bisa la'akari da babban fage mai ƙarfi na gwagwarmaya a duk faɗin yankin hakan ya ƙara takura da tsananta filin yaƙin ga Isra'ila da Amurka.
Har ila yau, gwagwarmayar Musulunci da gwarzon Iraqi sun gudanar da hare-haren makami mai linzami guda 19 a cikin sa'o'i da ta gabata. Bisa Dogaro da Allah Madaukakin Sarki, za a dauki fansar jinin duk wanda aka zalunta a duniya, musamman yara da wadanda ake zalunta a kasashen Gaza, Lebanon, Yemen, Iraki da sauran kasashen Musulunci, da makamai masu linzami da jirage marasa matuka na gwagwarmayar Musulunci. Tashar ta 12 ta ruwaito cewa, a daidai lokacin da Iran da Hizbullah da Yemen, sun harba makamai masu linzami ga Falasdinu da aka mamaye
Ita ma Yamen ta bayar da rahoton cewa: A wani aiki na hadin gwiwa da Iran da Hizbullah, mun kai hari kan yankunan da aka mamaye. Sojojin mu sun gudanar da aikin soja na biyar ta hanyar amfani da makamai masu linzami. Aikin ya kai hari kan filin jirgin saman Bangorion da ke Tel Aviv, da kuma muhimman wurare na sojojin Isra'ila a kudancin Falasdinu.
An gudanar da aikin ne tare da dakarun kare juyin juya hali, da sojojin Iran da kuma kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon, kuma da yardar Allah, ya samu nasarar cimma manufofinsa.
Your Comment