Sheikh Yakub Yahya Katsina : Ko ba komai idan aka ce Ali (AS) to magana ce ta ilmi, domin Manzon Allah (S) ya ce, shi ne magajin sa, shi ne ma kofar ilimin sa. "Ana Madinatul Ilmi, wa Aliyun babuha" Wannan sananne hadisi ne, mashhuri da kowa ya san shi, to kaga idan da mutum zai samu ilimi, kuma ilimin nan mai yawa, sai ace ta wace kofa ka shiga ka samu? sai aka bincika sai aka ga ba ta kofar Ali bane, to kila.... Wanda bai shiga ta kofa ba, to idan ya shigo ta bayan gida mai ya yi?
To ban sa ni ba ko ilimin... Zai iya zama halal? idan an... abu zai iya zama halal? Saboda haka kenan kaga indai ba a kofar Ali (AS) aka bi aka samu ba to wannan ilmin zai zama yana da alamar tambaya. Akwai wani ina tsammanin ko Abu Zarr (R) ne, yake tambayar Amirul-Mumunina (AS) cewa "Wai miyasa nike jin ilmummuka daban daban, idan naje cikin mutane sai inji wannan yace kaza, sai inji wane yace kaza, amma kai idan nazo sai inji ilimi sak.
Sai yace "A hannun mutane akwai bara-gurbin ilimi, akwai kuma sahihi, to ana gwamawa ne, a gauraya, sai mutane su faɗa cikin shubuha, su kasa gane daidai ba da daidai ba, saboda akwai gaskiya akwai ba gaskiya ba, sai a gwama, to wani lokaci mutum ya dace da daidai, wani lokaci kuma ya dace da ba daidai ba". Amma idan su ne ko ta hanyar shi Imam Ali (AS) da Manzon Allah (S) ya yi ma shi shaida, to kullum daidai zaka iske. Shiyasa wanda ya yi riko da Amirul-Mumunina Ali (AS) to ya dace, muna godiya ga Allah madaukakin sarki da ya haska mana.
Sannan kuma shi ilimin nan duk inda aka taru makarantu da zawiyoyi da cibiyoyin ilimi, zaka ji ana maganar ilimi, ilimi, ilimi. Saboda mi? Saboda ilimi ne gaba, ILMI KE SAMAR DA KOMAI na rayuwar duniya da rayuwar lahira da ilimi ne, hadda waɗanan ilmummukan na kire-kire. Akwai wani littafi ana ce mashi "Ku tambayi Ali (AS) ilimin farko da na karshe" ilimin farko da na karshe yana wajen sa an tara mashi, saboda haka babu abin da ya gagare shi wanda yake na ilimi ne. Har ma yana cewa "Ku tambaye Ni kafin ku rasa Ni ”.
Wannan wani bangare na jawabin Sheikh Yakub Yahya Katsina, a ranar Lahadi 13/08/1447, daidai da 01/02/2026, a wajen taron "YAUMU ALI" na bana, wanda ɗaliban Haidarori karkashin Lajnar Islamiyyu ta da'irar Katsina suke shiryawa a kowace shekara.
02/02/2026.
Your Comment