Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Jakadun sun bayyana cikakken goyon bayansu ga Sojojin Lebanon da kuma sadaukarwarsu wajen neman tsaro da kwanciyar hankali, suna mai jaddada muhimmancin ci gaba da kokarin Lebanon na aiwatar da tsagaita wuta da aka ayyana a ranar 26 ga Nuwamba, 2024.
Domin ci gaba da wadannan kokarin, mahalarta taron sun amince su kafa wata kungiyar aiki mai bangarori uku don shirya taron kasa da kasa don tallafawa Sojojin Lebanon da Jami'an Tsaron Cikin Gida, wanda aka shirya a watan Fabrairun 2026.
Your Comment