Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: A cewar wata sanarwa da Fadar White House ta fitar, Amurka ta sanya cikakken takunkumi kan shiga 'yan kasashen biyar, ciki har da Burkina Faso, Mali, Nijar, Sudan ta Kudu da Syria.
A cewar bayanan da aka buga a shafin yanar gizon Fadar White House, an kara wadannan kasashe biyar a cikin jerin kasashen da aka haramta masu shiga Amurka gaba daya.
Cikakken jerin kasashen da aka haramta shiga yanzu sun hada da Afghanistan, Burma (Myanmar), Chadi, Jamhuriyar Congo, Equatorial Guinea, Eritrea, Haiti, Iran, Libya, Somalia, Sudan, Yemen, Laos, Sierra Leone, Syria da kuma mutanen da ke dauke da takardun tafiya da Hukumar Falasdinawa.
Your Comment