25 Nuwamba 2025 - 09:52
Source: ABNA24
Wanene Haitham Tabtaba'I (Abu Ali) Babban Kwamandan Hizbullahi Da Isra'ila Ta Kashe A Kudancin Labnan?

Da yammacin ranar Lahadi a kudancin birnin ta Beirut, wani babban abin fashewa mai ƙarfi ya fashe, inda haramtacciyar ƙasar Isra’ila ta ce ita ce ta kai harin. Babban kwamandan dakarun Hizbullahi Hitham al-Tabtaba’i (Abu Ali al-Tabtaba’i), wanda shi ne mutum na biyu a Hezbollah bayan Shugaba Shaikh Naim Ƙaseem ya yi shahada wanda dama shi aka kaiwa wannan mummunan harin

Al-Tabtaba’i shugaba ne mai basira a harkokin soja, ya taimaka wajen gina ƙarfin rundunonin soja na Hizbullahi, ya jagoranci ayyuka masu yawan gaske a Siriya, kuma yana da alaƙa mai kyau tsakaninsa da Hukumar Iran da ta ƙasarsa Lebanon.

Amurka ta saka shi a jerin masu wanɗanda take nema ruwa a jallo, a duniya tare da alƙawarin bayar da tukuiwcin dala miliyan 5 ga duk wanda ya bayar da bayanai a akansa kamar yadda shafin Hukumar leƙen asirin Amurka CIA ta wallafa a shekarun baya.

Babban kwamandan na Dakarun Hizbullah “Hizbullah” na Lebanon, Haitham al-Tattabatai, yana daga cikin manyan shugabannin Sojin Hizbullahi da ke Lebanon guda biyar da suka taka muhimmiyar rawa a rikicin Yemen.

A yau Lahadi, Isra’ila ta kai hari da makami mai linzami kan muhallin da al-Tattabatai da ke cikin wani gida a unguwar Dahiyya kudu a birnin Beirut, in da ya yi shahada.

Wannan harin ya zo ne watanni bayan kisan wani babban jami’in A Sojin Hizbullahi Ahmad Saeed al-Hajj, a ƙarshen bara a Dahiyya, a yanayi makamancin haka, bayan shekaru yana aiki a matsayin jami’in ayyuka da kuma mai ba da shawara ga rundunarAnsrullahi a yaƙunan da suka gabatar da Saudiyya a shekarun baya.

Gudummawarsa Ga Dakarun Ansarullahi Na Yemen.

Al-Tattabatai, Wanda ake kira Abu Ali, ya taka rawar gani a Yemen ta hanyar wakiltar Hizbullah wajen tallafa wa Houthiyawa, da kuma jagorantar ƙwararrun Lebanawa da ke a can, baya ga jagoranci wajen tsara tallafin Iran—na kayan aiki da na soja—ga Ansarullahi.

A cewar majiyoyin soja na Yemen, Abu Ali al-Tattabatai ya isa Yemen ne a 2016, inda ya taimaka wajen gina tsarin tsaron kai na jagoran Houthi, Abdulmalik al-Houthi, tare da jami’an ƙuds Force na Iran da ke cikin ƙasar.

Majiyoyin sun tabbatar da cewa al-Tattabatai yana daga cikin manyan horasawa na musamman ga dakarun Houthi, ya kuma taka rawa wajen inganta ƙarfinsu na soja da na kayan aiki, har ma da tsara dabarun yaƙi daga filin daga har zuwa 2020.

Wani bincike na ABNA ya nuna cewa, Haramtacciyar ƙasar Isra’ila zuwan al-Tattabatai Yemen ya faro ne bayan ya tsira daga yunƙurin kisan da Isra’ila ta yi masa a 2015, wanda ya sa Hizbullah ya tura shi wajen gudanar da aiki na musamman wajen tallafa wa Ansarullahi na Yemen.

A shekarar da ta gabata, Isra’ila ta kashe manyan jami’an Hizbullah uku bayan dawowarsu daga Yemen—ciki har da shugaban rundunar sararin samaniya Muhammad Hassan Surur, wanda ya taka rawa wajen haɓaka karfin Ansarullahi a sararin samaniya, da Basil Shukr na rundunar “Ridwan”, da Ali Adel Ashmar, wanda ya daɗe yana aiki a Yemen a matsayin babban mai ba da shawara ga Houthi.

Cikin Isra'ila Ya Ɗuri Ruwa!

Isra’ila ta shiga cikin tashin hankali sakamakon kashe Abu Ali, a yayin da take jiran martanin Hizbullah kan kisan al-Tattabatai.

Farkon bayyana ƙwararrun Hizbullah da jami’an Iranian Revolutionary Guard a Yemen ya faro ne tun 2009, bayan an shigar da su ta ɓoye domin taimaka wa Ansarullahi a yaƙin su na shekara shida da Hukumar Saudiyya ta ƙaddamar a kan su bisa zalunci.

Daga Haj Emaad

Your Comment

You are replying to: .
captcha