Kafofin watsa labarai na Isra'ila sun bayyana cewa gina layin dogon sirri da ya haɗa Hadaddiyar Daular Larabawa da "Isra'ila" ya ci gaba a lokacin yaƙin Gaza. Aikin, wanda aka fi sani da "Layin Jirgin Ƙasa na Zaman Lafiya," yana da nufin haɗa Asiya da Turai ta hanyar Abu Dhabi, Saudiyya, Jordan, da Haifa.
Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa: Kafafen watsa labarai na Isra'ila, ciki har da Channel 15 da Yedioth Ahronoth, sun bayyana cewa aikin layin jirgin ƙasa na sirri da ya haɗa Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) da "Isra'ila" ya ci gaba har ma a lokacin yaƙin Gaza.
Tashar Channel 15 ta tabbatar da cewa gina layin jirgin ƙasa ya kai matakai na ci gaba kuma an gudanar da shi a ɓoye a duk lokacin yakin da ake fama da shi a Gaza.
Yedioth Ahronoth ta ba da rahoton cewa an farfaɗo da tattaunawa kan abin da ake kira "Layin Jirgin Ƙasa na Zaman Lafiya", wanda ya nuna wata tafiya ta sirri da Ministan Sufuri na Isra'ila Miri Regev ya yi zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa a makon da ya gabata don ganawa da jami'an Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma tattauna shirin.
An tsara aikin ne don ƙirƙirar hanyar kasuwanci da ta haɗa Asiya da Turai. Za a na jigilar kayayyaki daga Indiya zuwa Tashar Jiragen Ruwa ta Abu Dhabi, sannan ayi jigilar su ta jirgin ƙasa mai sauri ta cikin Hadaddiyar Daular Larabawa, Saudiyya, da Jordan, inda za su isa Tashar Jiragen Ruwa ta Haifa don rarrabawa zuwa Turai da Amurka.
An kuma cimma yarjejeniya don kafa hadakar gudanarwa ta haɗin gwiwa tsakanin manyan jami'ai daga Hadaddiyar Daular Larabawa da layin dogo na Isra'ila don kula da jigilar jiragen ƙasa. Wannan gudanarwar za ta kuma duba wata hanya ta daban da za ta ratsa tsakanin Jordan da "Isra'ila" ta cikin Tekun Bahril Mait na Kudancin don guje wa rikice-rikicen siyasa.
Your Comment