11 Nuwamba 2025 - 08:20
Source: ABNA24
Mutane 9 Sun Mutu Sanadiyyar Tashin Bom A Delhi Inadiya

Aƙalla mutane 9 sun rasa rayukansu bayan fashewar wani abu kusa da tashar jirgin ƙasa ta Lal Qala a babban birnin Indiya. Ba a tantance yanayi na fashewar ba tukuna.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa: Majiyoyin labarai na Indiya sun sanar da cewa wata fashewa ta faru a daren yau kusa da tashar jirgin ƙasa ta Lal Qala a New Delhi, kuma an tabbatar da mutuwar mutane 9 a lamarin zuwa yanzu.

Kafafen watsa labarai na Indiya sun ruwaito cewa fashewar ta faru kusa da Ƙofa Mai Lamba 1 ta tashar jirgin ƙasa ta Lal Qala a cikin wata mota. Ba a tantance nau'in fashewar da musabbabinta ba tukuna kuma ana ci gaba da bincike.

A cewar Sashen Kashe Gobara na Delhi, fashewar ta yi sanadiyyar kama motoci shida da kuma rickshaws uku. Jami'an kashe gobara sun sami nasarar shawo kan gobarar.

Kafafen watsa labarai na cikin gida sun ruwaito cewa an kai gawarwakin mutane 9 da lamarin ya rutsa da su asibiti. Ba a bayyana bayanai game da asalin waɗanda abin ya shafa da kuma yiwuwar adadin waɗanda suka ji rauni ba tukuna.

Jami'an tsaron Indiya sun sanar da cewa an fara gudanar da bincike na farko don gano yanayin fashewar da kuma yiwuwar harin ta'addanci ne.

........

Your Comment

You are replying to: .
captcha