Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa: hukumomin Lebanon sun sanar da cewa an saki Hannibal Gaddafi, dan tsohon shugaban Libya, daga gidan yari bayan ya bayar da beli na dala $900,000.
Wannan matakin ya kawo karshen tsare shi na shekaru 10 bisa zargin boye bayanai game da bacewar Imam Musa al-Sadr.
Charbel Milad Khoury, memba na tawagar kare Hannibal, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Associated Press (AP) cewa an sake shi ne a ranar Litinin da yamma bayan kammala ayyukan gudanarwa.
Jami'an tsaro biyu, wadanda suka yi magana ba tare da sun ambaci sunansu ba, sun tabbatar da labarin sakin dan Gaddafi. Sakin Hannibal Gaddafi ya zo ne kwanaki bayan da hukumomin Lebanon suka dage haramcin tafiye-tafiyensa tare da rage belinsa, wanda hakan ya share fagen sakinsa.
Your Comment