Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa: A karo na shida na zaɓen 'yan majalisar dokokin Iraki, an zaɓi 'yan takara 7,744 daga ƙungiyoyin haɗin gwiwa na zaɓe 31, kuma wakilai 329 daga ƙarshe za su je majalisar dokoki don tantance makomar siyasar ƙasar ta shekaru huɗu masu zuwa. 'Yan ƙasar Iraki sama da miliyan 21 ne suka cancanci kaɗa ƙuri'a a zaben.
Za a gudanar da zagaye na biyu kuma na ƙarshe na zaɓen 'yan majalisar dokokin Iraki daga ƙarfe 8 na safe a yau.
Your Comment