9 Nuwamba 2025 - 20:35
Source: ABNA24
Labanon: Mutane 28 Su Kai Shahada A Lebanon A Hare-Haren Isra'ila

Ministan Lafiya na Lebanon ya sanar da shahadar mutane 28 a cikin watan da ya gabata sakamakon hare-haren sama na Isra'ila a kasar.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na AhlulBaiti (As) –ABNA-ya habarta cewa: Ministan Lafiya na Lebanon ya sanar da shahadar mutane 28 a cikin watan da ya gabata sakamakon hare-haren sama na Isra'ila a kasar.

Hare-haren da gwamnatin mamaya ke kai wa Lebanon sun karu sosai a cikin 'yan watannin nan, musamman a yankunan kudancin kasar, har ta kai ga suna kai hare-hare da jirage sama marasa matuki ta sama a kudancin Lebanon sau da dama a rana.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha