10 Nuwamba 2025 - 08:28
Source: ABNA24
Hukumar Zaɓen Iraki: Kashi 82% Ne Suka Kaɗa Ƙuri'a A Zaɓen Musamman.

Shugaban Hukumar Kwamishinoni, Omar Ahmed, ya tabbatar a yayin wani taron manema labarai cewa an gudanar da zaɓen musamman cikin nasara da kwanciyar hankali, ba tare da an bayar da rahoton keta haddi ko kuma gazawar fasaha a cikin na'urorin lantarki ba. Ya lyi ishara da cewa Hukumar ta ci gaba da nuna rashin banbanci da rashin nuna son kai ga dukkan 'yan takara.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa: Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta sanar a jiya Lahadi 9 ga Nuwamba, 2025, rahoton ƙarshe kan zaɓen musamman a duk faɗin jihohin Iraki.

A cikin wannan yanayi, Shugaban Hukumar Kwamishinoni, Omar Ahmed, ya tabbatar a yayin wani taron manema labarai cewa an gudanar da zaɓen musamman cikin nasara da kwanciyar hankali, ba tare da an bayar da rahoton keta haddi ko kuma gazawar fasaha a cikin na'urorin lantarki ba. Ya lyi ishara da cewa Hukumar ta ci gaba da nuna rashin banbanci da rashin nuna son kai ga dukkan 'yan takara.

Ya ƙara da cewa adadin waɗanda suka halarci zaɓen musamman ya wuce masu kaɗa ƙuri'a miliyan 1.1, wanda ke daidai da kashi 82%.

Masu lura da al'amura sun yi imanin cewa wannan fitowar jama'a ta nuna cewa an fi son shiga babban zaɓe, tare da tsammanin cewa kaso zai fi yawa idan aka kwatanta da zaɓen da suka gabata.

.........................

Your Comment

You are replying to: .
captcha