29 Oktoba 2025 - 14:54
Source: ABNA24
Yadda Yunƙurin Kashe-Kai Ya Zamanto Ruwan Dare A Rundunar Isra'ila.

Rahoton da aka saki kwanan nan daga Cibiyar bincike da bayani ta Majalisar dokokin Isra’ila (Knesset Research and Information Center) ya bayyana wata matsananciyar matsalar lafiyar kwakwalwa a cikin sojojin IDF (Sojojin Tsaron Isra’ila):

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa: Majalissar dokokin Isra'ila (Knesset Research and Information Center) ta bayyana wani da ke cewa, an samu yunƙurin kashe kai 279 tsakanin Janairu 2024 zuwa Yuli 2025 ga dai bayanan filla-filla:-

1. Kashi 78% na waɗanda suka kashe kansu sojojin yaƙi ne, adadi wanda ya ninka kusan sau biyu idan aka kwatanta da kafin yaƙin.

2. Ga kowane soja ɗaya da ya kashe kansa, akwai sojoji bakwai da suka yi yunƙurin hakan.

Wannan hauhawar ta faru ne tare da babban kira na haɗa sojoji bayan harin 7 ga Oktoba — yaƙin da ya bar dubban sojojin ajin ajiye (reservists) cikin damuwa da rashin kwarin gwiwa tattare da sarewa.

Masana suna gargaɗi cewa, waɗannan alƙaluman sun haɗa ne da sojojin da ke aiki da na ajiye kawai, ba su haɗa da tsoffin sojoji da suka kashe kansu bayan sun bar aikin soja ba — ma’ana, gaskiyar asarar na iya zama mafi muni sosai.In ji rahoton.

Duniya dai tana ci gaba da ganin yadda kisan ƙare dangin da dakarun Haramtacciyar ƙasar Isra'ila ke yiwa al'ummar Palestinu bisa taimakon Shugaba Trump da wasu ƙasashe da suke aitawar da wannan ta'asa a tare. A yayin da ƙasashen Larabawa su ma suke bayar da gudummawa ga Isra'ila domin kawar da al'ummar Gazza daga rayuwa.

Rahoto: Haj Emaad

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha