Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa: Majalissar dokokin Isra'ila (Knesset Research and Information Center) ta bayyana wani da ke cewa, an samu yunƙurin kashe kai 279 tsakanin Janairu 2024 zuwa Yuli 2025 ga dai bayanan filla-filla:-
1. Kashi 78% na waɗanda suka kashe kansu sojojin yaƙi ne, adadi wanda ya ninka kusan sau biyu idan aka kwatanta da kafin yaƙin.
2. Ga kowane soja ɗaya da ya kashe kansa, akwai sojoji bakwai da suka yi yunƙurin hakan.
Wannan hauhawar ta faru ne tare da babban kira na haɗa sojoji bayan harin 7 ga Oktoba — yaƙin da ya bar dubban sojojin ajin ajiye (reservists) cikin damuwa da rashin kwarin gwiwa tattare da sarewa.
Masana suna gargaɗi cewa, waɗannan alƙaluman sun haɗa ne da sojojin da ke aiki da na ajiye kawai, ba su haɗa da tsoffin sojoji da suka kashe kansu bayan sun bar aikin soja ba — ma’ana, gaskiyar asarar na iya zama mafi muni sosai.In ji rahoton.
Duniya dai tana ci gaba da ganin yadda kisan ƙare dangin da dakarun Haramtacciyar ƙasar Isra'ila ke yiwa al'ummar Palestinu bisa taimakon Shugaba Trump da wasu ƙasashe da suke aitawar da wannan ta'asa a tare. A yayin da ƙasashen Larabawa su ma suke bayar da gudummawa ga Isra'ila domin kawar da al'ummar Gazza daga rayuwa.
Rahoto: Haj Emaad
Your Comment