Sheikh Naim Qassem ya kuma jaddada cewa mutane su ne masu matsayi na ɗaya a yaƙin gwagwarmaya, kuma ƙimarsu ta fi ta shugabanni da mayaƙan gwagwarmayar kansu. Ya nuna cewa ‘ya’yan Al’ummar da suke gwagwarmaya ba za’a kimanta su da wani abu ba, domin su ne waɗanda ke ƙarfafa tafarkin da kuma ƙara gwagwarmaya. Da ya fuskantar da jawabinsa ga mutane, ya ce, "Tare da ku, tafarkin yake ƙara ƙarfi, kuma ku muhimmin ɓangare ne na gwagwarmaya da nasarorin da ta samu".
Sheikh Qassem ya jaddada cewa Hizbullah ba ta fara yaƙi ba, sai dai ta ɗauki matakin kariya wanda ya dace daga maƙiyi da ke neman halaka mutane da mamaye ƙasar. Ya bayyana cewa idan ba a fuskanci hukumar Isra'ila ba, za ta ci gaba da faɗaɗawa da mamaye iko kuma za ta iya lalata makomar tsatso masu zuwa. Ya ƙara da cewa, "Ba mu ne ke jagorantar mutanenmu zuwa ga mummunan zaɓi ba, sai dai zuwa ga manyan zaɓe waɗanda ke kiyaye mutunci da kuma kafa makoma mafi kyau".
Ya kuma jaddada cewa babu wani daukaka a yankin sai ta hanyar gwagwarmaya, kuma rashin daidaiton iko a yanzu yana wakiltar wani mataki wanda ba za a iya raba shi da matakan da suka gabata na gwagwarmaya da juriya ba. Ya jaddada cewa zabin ayi gwagwarmaya shine zabi na dole don kare kasa da mutane da kuma tabbatar da mutuncin kasa ga tsatso masu zuwa.
Your Comment