Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Ofishin yada labarai na gwamnatin Falasdinu a Gaza ya sanar a yau Asabar cewa ‘yan mamaya sun karya yarjejeniyar tsagaita wuta har sau 47 tun bayan kawo karshen yakin yankin.
Ofishin yada labarai na gwamnati a Gaza ya bayyana cewa: "Ayyukan keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta sun hada rashin kawo karshen yakin da kuma keta ka'idojin dokokin jin kai na kasa da kasa, ciki har da harbe-harbe kai tsaye kan fararen hula, hare-haren ganganci da kuma kama wasu fararen hula".
A cikin wata sanarwa da ofishin ya fitar ya ce: An kai wadannan hare-hare ta hanyar amfani da motocin soji da tankokin yaki da aka ajiye a kusa da wuraren zaman fararen hula tunbobin lantarki, inda suka kai hare-haren da iragen sama marasa matuka (quadrocopters) wadanda ke ci gaba da shawagi a kan wuraren zama tare da bude masu.
Ofishin yada labarai na gwamnati a Gaza ya sanar da cewa, an bibiyi wadannan laifukan a dukkan yankunan zirin Gaza ba tare da togiya ba, lamarin da ke nuni da cewa gwamnatin yahudawan sahyoniya ba ta dauki wani mataki na dakatar da wuce gona da iri ba, tana mai dagewa kan ci gaba da manufofinta na kisa da ta'addancin al'ummar Palastinu.
Sanarwar ta ce, an samu shahidai 38 da kuma jikkata 143 a sakamakon wannan hare-hare na cin zarafi da ake ci gaba da yi tun bayan yanke yarjejeniyar dakatar da yakin har zuwa yau.
Sanarwar ta ce: "Mun dora alhakin wannan hare-hare ga 'yan mamaya a cikin wannan lamari, muna kuma kira ga Majalisar Dinkin Duniya da masu shiga tsakani cikin gaggawa domin tilastawa Isra'ila dakatar da ci gaba da kai hare-hare da kuma kare fararen hula marasa tsaro a zirin Gaza".
Your Comment