Kamfanin dillancin labarai na AhlulBaiti (ABNA): Ma’aikatar lafiya ta Gaza ta bayar da rahoton cewa sama da Falasdinawa 68,000 ne aka kashe tun daga ranar 7 ga watan Oktoban 2023, baya ga wasu da dubbai da suka jikkata ko suka bace, yayin da har yanzu sakamakon kawanyar ba a samu kai kayyakin agaji ba yadda suka kamata.
Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya sun yi gargadi game da hadarin yunwa da durkushewar ayyuka masu muhimmanci, inda WHO da UNICEF suka bayar da rahoton kai hare-hare akai-akai kan ababen more rayuwa na fararen hula, da suka hada da asibitoci da makarantu.
A watan Janairun 2024, Kotun Duniya ta tabbatar da yiwuwar kisan kare dangi tare da ba da umarnin daukar matakan gaggawa don kare Falasdinawa a Gaza.
Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana yin Allah wadai da wuce gona da iri na gwamnatin sahyoniyawan kasar, tare da yin kira da a tsagaita bude wuta cikin gaggawa da kai kayan agaji ba tare da bata lokaci ba, da kuma hukunta masu aikata laifukan ta’addancin na kasa da kasa.
Your Comment