27 Nuwamba 2025 - 20:52
Source: ABNA24
Shekh Zakzaky Ha Aike Da Sakon Ta'aziyyar Rashin Shekh Ɗahiru Usman Bauchi

Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki da Ya saukar da rahamarsa ga ruhin marigayin; Ya sanya aljanna ta zama makomarsa ta har abada; sannan kuma Ya ba wa iyalansa da masoya haƙuri da juriyar wannan rashi. 

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحيم

إنا لله وإنا إليه راجعون 

يَا أَيَّتُهَا النَّفْسُ الْمُطْمَئِنَّةُ, ارْجِعِي إِلَىٰ رَبِّكِ رَاضِيَةً مَرْضِيَّةً, فَادْخُلِي فِي عِبَادِي, وَادْخُلِي جَنَّتِي

Sakon yazo kamar haka:

Labarin rasuwar babban Malami Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi (R), yau Alhamis 06/Jimada Ath-Thaniyah/1447, ta sanya masoya cikin damuwa da jimami. 

Marigayi ya kasance daya daga cikin fitattun malamai wanda ɗalibai da malamai suka amfana da tarin iliminsa. 

Wannan babban rashi ne ga daukacin al'ummar musulmi, Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) na mika sakon ta'aziyyarsa ga Iyalai da ɗalibansa masu daraja. 

Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki da Ya saukar da rahamarsa ga ruhin marigayin; Ya sanya aljanna ta zama makomarsa ta har abada; sannan kuma Ya ba wa iyalansa da masoya haƙuri da juriyar wannan rashi. 

06/Jimada Ath-Thani

Sheikh Sharif Saleh ne zai yi wa Sheikh Dahiru Bauchi jana'iza kamar yadda ya yi wasiyya 

Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Alhusaini na garin Maiduguri ne zai jagoranci sallar jana'izar Marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi kamar yadda ɗan marigayin, Dakta Abubakar Surumbai ya bayyana cewa ya bar wasiyyar hakan.

27/11/2025

Allah Ta'ala Ya Gafarta Masa Da Rahamarsa 

Your Comment

You are replying to: .
captcha