Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa: Ministan harkokin wajen Cuba ya ce: Washington tana son boye ainihin burinta na mamaye ma'ajiya da taskar man fetur ta Caracas a bayan wannan ikirarin karyan nata.
Ya ci gaba da cewa danganta shugabancin "Cartel de los Soles" ga shugaban Venezuela Nicolás Maduro da sanya sunan kungiyar a cikin jerin kungiyoyin ta'addanci makirci ne da hukumomin leken asiri na Amurka suka kirkira, kuma ya jaddada: Da wannan matakin, Washington na neman hujjar cin zarafin soja a kan Latin Amurka da yankin Caribbean da kuma komawa ga siyasar jiragen ruwa na wannan yanki
Your Comment