5 Oktoba 2025 - 21:46
Source: ABNA24
Gagarumin Bukin Bude Makarantar Markazul Al-Mustafa (S) A Tanzaniya + Hotuna

Bude makarantar koyon sana'o'i da koyon addini ta Markaz Al-Mustafa ana daukarsa a matsayin wani muhimmin matakin bunkasa cibiyoyi na Musulunci a kasar Tanzaniya wajen shirya matasan da suka hada ilimin zamani da koyarwar Musulunci.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlulbayt {As} –ABNA- ya bayar da rahoton cewa: an gudanar da gagarumin bukin bude makarantar koyar da sana’o’in hannu da addini ta Markaz Al-Mustafa cikin nasara a garin Moshi dake yankin Kilimanjaro.

Ita dai wannan sabuwar makaranta an kafata ne domin ta kasance cibiya ta ilimi da za ta baiwa matasa damar samun ilimin fasaha da kuma ilimin addini, da nufin gina al’umma mai fahinta, ilimi da kyawawan dabi’u na Musulunci.

Taron ya samu halartar manyan baki daga cibiyoyin addinin musulunci daban-daban, iyaye, dalibai, da al'ummar yankunan da ke kewaye. An gudanar da bikin ne ta hanyar rarraba takaddun shaida ga daliban da suka kammala karatunsu, alamar fara tafiya ta ilimi a hukumance tare da mai da hankali kan ruhiyya da ci gaba.

Babban bako a wajen taron shi ne, Sheikh Salmani Mwagwe, jagoran Mu’assasar Ahlul-Bait (as) na gabashi da tsakiyar Afirka, wanda a nasa jawabin ya jaddada muhimmancin hada ilimin duniya da ilimin addini. Yace: "Musulunci yana karfafa ilimi ga kowa-da-kowa-ilimin da ke gina mutum ta fuskar tarbiya da fasaha. Ya kamata matasanmu su kasance gwanayen ilimi, kirkire-kirkire da kuma takawa a cikin al'ummominsu".

A nasu bangaren, shugabannin Markaz Al-Mustafa sun nuna godiya ga duk masu ruwa da tsaki da suka bayar da gudumawarsu wajen ganin an samu nasarar gina makarantar da kafa makarantar, inda suka yi alkawarin ci gaba da kokarin samar da ingantaccen ilimi bisa gaskiya, ilimi da mutunta addini.

Bude makarantar koyon sana'o'i da addini ta Markaz Al-Mustafa ana daukarsa a matsayin wani muhimmin mataki na ci gaba da bunkasa cibiyoyi na addinin musulunci a kasar Tanzaniya wajen shirya tsararrun matasa masu hada ilmin zamani da addinin Musulunci.

Your Comment

You are replying to: .
captcha