Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlulbayt {As} –ABNA- ya bayar da rahoton cewa: babban kwamandan rundinar Qudus ya bayyana cewa: Muna yaki mai sarkakiya a birnin Gaza, kuma makiya suna yin amfani da kwarewarsu domin rama asarar da suka yi a baya domin rage hasarar da suke yi, muna da mayaka jarumai wadanda su ne babban birninmu a kowane lokaci, kuma tare da su muna fuskantar makiya tare da farmasu a duk lokacin da dama ta samu da makaman da suka da ce, kuma Allah ya datar da mu ta hanyar aiwatar da wasu ayyuka na jarumta’ makiya ako yaushe sun aikata karya da yaudara game da hasarar mutanensu".
Ya kara da cewa "ci gaba da shigowar makiya zuwa tsakiyar birnin Gaza yana faruwa ne a karkashin idanun mayakan mu na gwagwarmaya, muna da dabarun da takensu shi ne "Ababen Farauta Masu Tsoka" wanda mafi yawan sojojin makiya da aka kashe da kuma jikkata su tarkon ya shafa. Muna kuma shaida wa sojojin makiya cewa ba mu da nisa da ku, kuma za ku ga fuskokinmu a duk lokacin da muka yanke shawarar yin hakan, saboda muna gudanar da yaki mai tsatsanani da sarkakiya kuma mun san dabarunmu farin sani".
Kwamandan rundunonin Quds ya jaddada cewa, makiya ba za su samu wurin tsira ba a Gaza, na'am, zasu iya ci gaba wajen shigowa, amma asarar hakan makiya sun santa.
Kwamandan runduna ta Kudus ya kammala da cewa, "Sakonmu zuwa ga Al’ummarmu masu jihadi masu hakuri, shi ne cewa muna jin radadin kuke ji, kuma a kodayaushe muna kokarin ganin cewa wannan ta'addancin ya zamo mai tsadar farashi ga makiya, muna sumbatar kan kowane daya daga cikin al'ummarmu, kuma in sha Allahu hakurinmu na hadin gwiwa zai ba da sakamako cikin daukaka da alfijirin nasara nan kusa".
Gidan rediyon sojojin Isra'ila ya bayar da rahoton cewa, a halin yanzu rundunoni uku da ke fafatawa a birnin Gaza sun tsaya cik a wuraren da suke zaune, ba tare da wani ci gaba da mamaye fagen daga ba, sannan basu janye ba. A nata bangaren, jaridar Isra'ila Hayom, ta nakalto majiyar siyasar Isra'ila, ta bayar da rahoton cewa, dakatar da hare-haren da sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila suke yi a zirin Gaza da nufin baiwa Hamas damar fara shirye-shiryen sako sojojin da aka yi garkuwa da su ne.
Idan dai ba a manta ba a yammacin jiya ne kungiyar Hamas ta sanar da mika martaninta ga shirin shugaban Amurka Donald Trump na dakatar da yakin zirin Gaza ga masu shiga tsakani.
Dangane da matakin da Hamas ta dauka na amincewa da shawararsa na dakatar da yakin Gaza, Shugaba Trump ya sanar da cewa kungiyar a shirye take ta samar da zaman lafiya mai dorewa, yana mai neman Isra'ila ta gaggauta dakatar da kai hare-hare a Gaza.
Your Comment