Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Ahlul Baiti (A.S.) - ABNA - daga Beirut ya ruwaito; Shekara guda kenan da shahadar shugaban gwagwarmayar Sayyid Hasan Nasrallah a yau a Beirut babban birnin kasar Labanon, ta cika makil don raya tunawa wannan babban rashi na mujahidai.
A cikin 'yan sa'o'i kadan al'ummar birnin Beirut da magoya bayan gwagwarmysa sun yi tururuwa zuwa wannan taro ta hanyoyi daban-daban don girmama tunawa da Sayyid shugaban wadanda aka zalunta tare da sake sabunta kudurinsu kan tabbata kan manufofinsa.
An shirya matakai na musamman don ganin wannan taro ya kasance mai girma da bajinta kamar yadda ya kamata, kuma za a gudanar da waƙoƙin zaburantarwa n jihadi a wurin.
Bikin wanda aka fara a mintuna kadan da suka gabata da karatun kur'ani mai tsarki, ya samu halartar Ali Larijani, babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran, da tawagar kasar Iran.
Hujjatul Islam Walmuslimin Qomi, Shugaba mai kula da harkokin kasa da kasa na ofishin Jagoran juyin juya halin Musulunci da Ayatullah Mohsen Araki, mamban majalisar koli ta majalisar Ahlul Baiti (AS) ta duniya da wasu gungun jami'an kasar Iran ne suke tare da tawagar.
Da saukar Dr. Larijani a takaice ya gana da mahaifin Shahidi Nasrallah.
Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sheikh Naim Qassem zai yi jawabi a wajen taron.
Jami'an kasar Lebanon da na sauran kasashe da dimbin jama'a ne ke halartar taron, kuma daruruwan 'yan jarida da masu fafutukar yada labarai ne ke yada labarai.
Har ila yau a wajen bikin akwai Hujjatul Islam Walmuslimin Moinian, shugaba jami'I mai kula da harkokin kasa da kasa, Hujjatul Islam Walmuslimin Imamzadeh, babban darakta mai kula da harkokin Afirka da larabawa, da Hujjatul Islam Walmuslimin Nakhaei, shugaban ofishin wakilan majalisar Ahlul Bayt (AS) ta duniya a kasar Lebanon, mai wakiltar majalisar Ahlul Bayt (AS) ta kasar Lebanon.
A shekarar da ta gabata a rana irin ta yau, Gwamnatin sahyoniyawan yahudawa ta kai wani hari mafi girma a birnin Beirut, wanda sakamakon harin Sayyid Hasan Nasrallah, babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon, tare da wasu kwamandojin Hizbullah da dama, da kuma Janar Abbas Nilforoshan, kwamandan dakarun kare juyin suka yi shahada.
Your Comment