Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: A jiya Alhamis ne aka gudanar da taro na hudu na ministocin harkokin wajen kasashen Sin da Iran da Pakistan da kuma Rasha a gefen taron MDD karo na 80 da ake yi a birnin New York.
A cikin sanarwar ta karshe, kasashen hudu sun jaddada goyon bayansu ga kasar Afganistan mai cin gashin kanta, da hadin kai da dunkulewar kasar, ba tare da samuwar ta'addanci ko yaki ko safarar miyagun kwayoyi ba.
Bangarorin sun bayyana matukar damuwarsu game da yanayin tsaro a Afghanistan, duba da kasancewar kungiyoyi irinsu ISIS, Al-Qaeda, Tehreek-e-Taliban Pakistan (TTP), Jaish-ul-Adl, Balochistan Liberation Army (BLA) da sauran kungiyoyi makamantan su a matsayin babbar barazana ga tsaron yankin da ma duniya baki daya.
Sun kuma jaddada cewa, karfafa zaman lafiya da yaki da ta'addanci, tsatsauran ra'ayi, da laifukan da suka shafi muggan kwayoyi a Afganistan, na cikin moriyar anfani da zai sami kasashen yankin baki daya.
Your Comment