A cikin batu na uku na jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musuluncin yayin da yake ishara da mabambantan ra'ayoyi da 'yan siyasa kan batun "tattaunawa da Amurka" ya ce: "Wasu na ganin yin tattaunawa da Amurka na da amfani, wasu kuma na ganin cewa abu ne mai cutarwa, amma ina tunatar wa al'ummar kasar abin da muka fahimta da kuma abin da muka gani tsawon shekaru, sannan ina kuma son jami'ai da masu fafutuka na siyasa da su yi tunani da nazari kan wadannan batutuwa da kuma yanke hukunci na gaskiya".
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Mai yiyuwa ne a nan gaba wani yanayi na daban ya samu, misali shekaru 20 ko 30 daga yanzu, to amma a halin da ake ciki yanzu, tattaunawa da Amurka abu ne marar amfani, wanda kwata-kwata ba ya taimaka wa moriyar kasa, kuma ba ya kare wata barna daga kasar, sai dai ya haifar da cutarwa mai girma, wani lokacin ma ba za a iya gyara barnar da ya haifar ba.
Yayin da yake bayyana rashin amfanin yin tattaunawa da Amurka, ya ce: Bangaren Amurka ya riga ya tantance sakamakon tattaunawa ta hanyar nasa ra'ayin, ya kuma bayyana cewa, yana son yin tattaunawar da zata haifar da "dakatar da ayyukan nukiliya da kuma kara habakar sinadarin a cikin kasar Iran".
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kira zama a kan teburin irin wadannan tattaunawar wata alama ce ta karbar umarni, da tilastawa, da cin zarafi daga wani bangaren, ya kuma kara da cewa: A yanzu haka ya ce dakatar da wadatar sinadrin Uranium ne kwai suke bukata, amma mataimakinsa a kwanakin baya ya ce bai kamata Iran ta kasance tana da makamai masu linzami masu matsakaici da gajeren zango ba, yana nufin cewa hannayen Iran za a daure su Kenan ya zamo bata da komai, ko da kuwa an kawo mata hari ba zata iya mayarda martani ba kenan, ya zamo ba zata iya kai hari hatta a sansanin Amurka da ke Iraqi ba ko wani wuri daban.
Ya dauki irin wannan fata da maganganun da jami'an Amurka suka yi a matsayin sakamako na rashin masaniyarsu ga al'ummar Iran da Jamhuriyar Musulunci, da kuma rashin sanin falsafa da asasi da alkiblar Iran din, ya ce: Kamar yadda mu al'ummar Mashhad suke cewa wadannan kalmomi sun fi karfin bakin mai magana kuma ba su cancanci kulawa ba.
Ayatullah Khamenei bayan ya bayyana rashin amfanin yin tattaunawa da Amurka, ya ci gaba da bayyana irin illoli da suke tattare da yin ta, yana mai cewa: Daya bangaren kuma ya yi barazanar cewa idan ba ku yi tattaunawa ba, to kaza da kaza zai faru. Don haka yarda da irin wannan tattaunawar wata alama ce ta karba da yarda da barazana, tsoro, firgita, da mika wuya ga al'umma da kasa ga barazana.
Ya ce mika wuya ga barazanar Amurka ce dalilin ci gaba da nemanta ga wasu bukatun na tilas da basu da iyaka, inda ya kara da cewa: A yau suna cewa idan kuna da wadatar sinadarin Uranium za mu yi kaza da kaza, kuma gobe za su yi amfani da mallakar makamai masu linzami bisa alakan shi da mallaka ko rashin mallakar wata kasa a matsayin tushen barazana da kuma tilasta musu ja da baya.
Ayatullah Khamenei ya nanata cewa: Babu wata al'umma mai daraja da za ta yarda da tattaunawa tare da barazana, kuma babu wani dan siyasa mai hikima da zai yarda da hakan.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kira wa'adin da wani bangaren ya yi na rangwame da sassauci idan aka amince da bukatunsa da cewa na karya ne kawai, yayin da yake ishara da kwarewar JCPOA, ya ce: "Shekaru 10 da suka gabata, mun sanya hannu kan wata yarjejeniya da Amurkawa, bisa ga cewa za a rufe cibiya daya ta samar da makamashin nukiliya, kuma za a fitar da kayayyakin da aka zuwa a kasashen waje, ko kuma a saukaka tasirinsu, a maimakon hakan kuma za a dage takunkumin da aka kakabawa Iran".
Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: Tabbas na shaida wa jami'ai cewa shekaru 10 yayai tsayi daidai yake da rayuwa, me ya sa kuka amince da hakan, ya kamata a ce ba za su aminci da shi ba, amma sun amince, amma a yau da wadannan shekaru 10 din suka wuce, ba wai kawai ba a daidaita lamarinmu na nukiliya ba, sai dai ma matsalolin hakan sun karu a kwamitin sulhu da hukumar Nokliya.
Yayin da yake ishara da watsi da alkawurran da Amurka ta dauka na dage takunkumi, da ficewa daga kungiyar ta JCPOA, ko kuma yadda jama’a suke cewa: yaga takardar JCPOA duk da zartar da alkawurran da Iran ta yi, ya ce: "Haka daya bangaren yake, kuma idan kuka yi tattaunawa da shi, kuma kuka amince da bukatunsa, to hakan zai kai ga mika wuya ga kasa durkushewar daukakar al’umma, kuma idan ma baku karba ba zai yada wadannan barazanar ce da a halin yanzu yake aiwatarwa”.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi la'akari da cewa bai kamata a manta da abubuwan da kasar ta samu ba, ciki har da abubuwan da suka faru a cikin shekaru 10 da suka gabata, ya kuma kara da cewa: A halin yanzu, ba ni da niyyar tada wasu batutuwa da kasashen Turai, amma daya bangaren, Amurka, tana karya alkawuran da ta yi, da yin karya a cikin komai, ta kan yi barazanar soji daga lokaci zuwa lokaci, kuma idan ta samu dama, to za ta iya kashe mana mutane, irinsu Janaral Sulaimani Aziz, ko kuma ta yi ruwan bama-bamai ga wasu cibiyoyin na mu. Shin zai yi yin tattauanwa da irin wannan banagren cikin cikakken aminci ko ma ya zamo a iya yin alkawari da shi?”
Ayatullah Khamenei ya nanata cewa: Tattaunawa da Amurka kan batun nukiliyar da ma wasu batutuwan, wani lamari ne da ba zai cimma matsaya ba.
Tabbas ya yi la'akari da yin tattaunawa da Amurka abu ne mai amfani ga shugaban kasa mai ci, kuma wata hanya ce ta nune kawai da kare barazanarsa na da tasiri da kuma kai Iran kan teburin tattaunawa, ya kuma sake cewa: To Amma Wannan Tattaunawar Cutarwa Ce Tsagoranta, Kuma Ba Za Ta Haifar Da Wata Fa'ida Ba.
A karshen jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa, hanya daya tilo ta magance matsaloli da ci gaban kasar ita ce kara karfi a dukkan bangarori na soja, ilimi, gwamnati, tsari, sannan ya kara da cewa: Wajibi ne masu hankali da kwararru masu kulawa su nemo tare da bin hanyoyin da za su karfafa kasar, domin idan ta yi karfi to dayan bangaren ba zai kara yin barazana ba.
Ayatullah Khamenei yana ganin ya wajaba a dogara ga Allah da kuma yin tawassuli da tsarkakan Imamai wajen jawo taimakon Ubangiji, ya kuma kara da cewa: Wajibi ne mu ciyar da al'amura gaba ta hanyar gabatar da kokarin kasa a gaba, kuma za a yi hakan da samun nasarar Ubangiji.
Your Comment