25 Satumba 2025 - 10:47
Source: ABNA24
Jagora: Ba Mu Mika Wuya Ga Amurka Ga Batun sinadarin Uranium Ba, Ko Ga Matsin Lamba A Akan Wani Lamari Ba.

A kashi na biyu na jawabinsa ga al'ummar kasar, Jagoran juyin juya halin Musulunci yayin da yake ishara da maimaita kalmar wadatar sinadarin Uranium a fagen siyasa da na waje ya ce: Wajibi ne mu fahimci dalilin da ya sa wannan lamari yake da muhimmanci ga makiya.

A kashi na biyu na jawabinsa ga al'ummar kasar, Jagoran juyin juya halin Musulunci yayin da yake ishara da maimaita kalmar wadatar sinadarin Uranium a fagen siyasa da na waje ya ce: Wajibi ne mu fahimci dalilin da ya sa wannan lamari yake da muhimmanci ga makiya.

Da yake gayyatar masana da su yi bayani kan girma da fa'idar bunkasar sinadarin Uranium, ya ce: A wajen ingantawa, masana kimiyya da masana suna mayar da sinadarin Uranium da ake hakowa daga ma'adinan kasar, ta hanyar hadaddun kokarin fasaha na zamani, zuwa wani abu mai matukar kima, mai wadataccen sinadarin uranium, wanda ke da anfani wajen aikace-aikace da yawa a fannoni daban-daban da kuma rayuwar mutane.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da anfanin sinadarin Uranium wajen aikace-aikace daban-daban a fannin noma, masana'antu da kayayyaki, muhalli da albarkatun kasa, kiwon lafiya, abinci mai gina jiki, bincike da ilimi, Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: A fannin samar da wutar lantarki, amfani da sinadarin uranium da aka inganta shi ma yana da rahusa sosai kuma baya gurbata muhalli, kuma kamfanonin makamashin nukiliya suna da tsawon rai da fa'ida masu yawa. Don haka ne kasashe da dama da suka ci gaba ke amfani da tashoshin makamashin nukiliya, amma man da ake amfani da shi wajen samar da wutar lantarkin namu galibin man fetur ne da iskar gas wanda ke da tsada sosai.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin yayin da yake bayyana yadda ake samar da masana'antu a kasar nan, ya ce: Ba mu da wannan fasaha, wasu kasashen kuma ba su biya bukatunmu ba a wannan bangaren, amma bisa kokarin wasu kwararrun manajoji da manyan jami'ai, mun fara motsi shekaru talatin ko fiye da haka, kuma a yanzu mun shiga wani mataki na wadata sinadarin Uranium.

Yayi Magana dangane wasu kasashe da suke ganin wadatar sinadarin Uranium har zuwa kashi 90%  na Iran na nufin kera makaman kare dangi da ya ce: Mu Tun da ba mu da makaman nukiliya, kuma ba mu yi yunkurin kerawa ko amfani da wadannan makaman ba, shi yasa muka kara habaka shi zuwa kashi 60%, wanda hakan yana da kyau matuka.

Ayatullah Khamenei ya bayyana Iran a matsayin daya daga cikin kasashe 10 da suke da masana'antun inganta sinadarin Uranium a tsakanin kasashe sama da 200 na duniya inda ya ce: Baya ga ci gaban wannan fasahar zamani, muhimmin aikin masana kimiyyar mu shi ne horar da ma’aikata; ta yadda a yau dimbin masana kimiyya da furofesoshi, daruruwan malamai da dubun dubatar ma’aikatan da aka horar da su a fannonin da suka shafi nukiliya, suna aiki da kokari; sannan makiya suna tunanin cewa ta hanyar jefa bama-bamai a wasu wurare ko kuma yin barazana zai iya lalata wannan fasaha a Iran.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da matsin lamba na tsawon shekaru da dama da azzalumai suka yi na ganin al'ummar Iran ta mika wuya, sannan kasar ta kau da kai daga wadatar sinadarin Uranium, ya jaddada cewa: Ba mu mika wuya ba kuma ba za mu yi ba, kuma ba za mu mika wuya ga matsin lamba a wani lamari na daban ba.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce: Amurkawa sun kasance suna cewa bai kamata ku kasance kun mallaki wadatar sinadarin Uranium mai yawa ba, kuma ku rika fitar da kayayyakin da aka inganta zuwa wajen Iran; amma yanzu bangaren Amurka ta sanya kafarta cikin takalmin  karfe da su ke cewa bai kamata ku samu wadatar komai ba.

Ya jaddada cewa: Ma'anar wannan zalunci shine ku watsar da wannan babbar nasara da kuka samu tare da saka hannun jari da ƙoƙari ga iska; amma al'ummar Iran masu kishi ba su yarda da hakan ba, kuma sun naushe bakin mai wannan maganar.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha