Shahid Sayyid Hasan Nasrallah Daga Bakin Diyarsa Daya Tilo + Bidiyo

Shahidi Nasrallah Daga Kalaman Diyarsa | Hira Ta Musamman Da Sayyidah Zainab Sayyid Hasan Nasrallah
25 Satumba 2025 - 15:49
Source: ABNA24
Shahid Sayyid Hasan Nasrallah Daga Bakin Diyarsa Daya Tilo + Bidiyo

Kafar yada labarai ta Asr ta buga hira ta farko ta musamman tare da Zainab Nasrallah, diyar shahidi Sayyed Hassan Nasrallah.

Kamfanin dillancin labaran Ahlulbayt na kasa da kasa (ABNA) ya bayar da rahoton cewa: a karon farko tun bayan shahadar Sayyid Hasan Nasrallah, babban sakataren kungiyar Hizbullah a kasar Labanon, Kafar yada labarai ta Asr ta yi wata tattaunawa ta musamman da diyarsa daya tilo mai suna Zainab Nasrallah. Wanda dan jarida kuma kwararre kan al'amuran Lebanon Hussein Pak ne ya gudanar da hirar.

A cikin wannan hirar, Zainab Nasrallah ta tattauna batutuwan rayuwar mahaifinta da ba a bayyana su ba a matsayinsa na uba da miji da kuma danginsa, ta kuma gabatar da wani fuska da ba kasafai ake ganin irinta ba ta shahidi Sayyid Hasan Nasrallah.

Har ila yau, wani bangare na hirar ta kebenta shi ne da yin bayanin yadda take kallon abubuwan da suka faru a kasar Labanon da kuma matsayin da mahaifinta ya gadar ga a ra'ayin jama'ar yankin.

Game da Shahidi Nasrallah daga Kalmomin Diyarsa Kadai

Shahidi Nasrallah Daga Kalaman Diyarsa | Hira Ta Musamman Da Sayyidah Zainab Sayyid Hasan Nasrallah

Wannan tattaunawa ita ce labarin farko a hukumance da kafafen yada labarai su kayi tare da iyalan Sayyid Hassan Nasrallah bayan shahadarsa, wanda aka gabatar wa masu sauraro a matsayin wata tattaunawa ta musamman da 'yarsa, Malama Zainab Hasan Nasrallah. Muhimmancin wannan hirar ba wai a matsayin dangin wanda aka yi hira da shi kadai ba ne, har ma da sabbin abubuwa da ba a san su ba da ta ke nuna irin hali da halayen jagoran gwagwarmayar Lebanon.

Zainab Hassan Nasrallah Ta Yi Magana Game Da Rayuwar Mahaifinta A Karon Farko

Muhimmancin wannan hirar shi ne cewa a karon farko wakilin iyalan Shugaban Shahadan gwagwarmaya ya yi magana kai tsaye ga ra'ayin jama'a tare da bayyana wasu al'amurran shahidin da ba a cika ganin su ba har zuwa yanzu.

A cikin wannan hirar, Sayyidah Zainab Sayyid Hasan Nasrallah ta yi ishara da fannonin rayuwar mahaifinta, ruhiyyarsa, da halayensa a cikin iyali a karon farko.

Ta gabatar da wata fuska ta hakikanin mutum na kusa na Sayyidush Shahada; Mutumin da, baya ga zama shugaban siyasa da na soja, kuma yana da halaye na musamman na ’yan Adamtaka a matsayinsa na uba, miji ga iyali.

Wani muhimmin bangare na wannan tattaunawa ta bayyana ci gaban tafarkin gwagwarmya bayan shahadar Sayyid Hasan Nasrallah. A cikin wannan yanayi, Sayyida Nasrallah, tana mai jaddada matsayin mahaifinta na ilimi da na aikace, tana magana ne kan ci gaba da tafarkin gwagwarmaya da biyayya ga manufofin da ya yi riko da su, da mahangar Sayyid Hasan Nasrallah dangane da yakar Isra'ila, da yadda yake mu’amala al'ummar musulmi da wand aba musulmi ba na Lebanon da kasashen yankin, da batun hadin kan Shi'a da Sunna da dai sauransu.

Wannan hirar ta kasance mataki-mataki ne tattaunawa da Sayyidah Zainab Hasan Nasrallah na sirri da na nazari kan mahaifinta, inda a lokaci guda ti yi nuni ga wasu bangarori na tunani da siyasa na dabi’ar Sayyid Hasan Nasrallah. An buga wannan aikin ne kawai akan dandalin Asr TV.

Mun kawo maku wani yanki na farko don haka masu sha'awar za su iya duba cikakkiyar hirar ta kafar gidan yanar gizon Asr a wannan hadin: asrtv.com

Your Comment

You are replying to: .
captcha