Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– Ya Kawo maku jawabin da Hujjatul-Islam WalMuslimeen, Sayyid Abdul Fattah Nawwab Wakilin Jagoran Harkokin Hajji da ziyara yayi a wajen rufe taron bikin ‘yan jaridu na kasa da kasa mai taken: (Mu Ƴaƴan Husaini Ne) karo na biyu ya jaddada wajibcin samun cin gajiya da anfana da kalaman Imam Husaini (AS) da kuma bayyana salon rayuwar Imam Husaini (AS) a cikin shirye-shiryen kafafen yada labarai wanda aka gudanar a Majma'a Yavaran Mahdi As Jamkaran.
A wajen bikin ya bayyana cewa: “A cikin wannan taro, dole ne mu amfana da maganar Imam Husaini (AS), wanda wadannan kalmomin a tsawon tarihi suna raye har abada, kuma wajibi ne a yi amfani da su a koda yaushe.
Dangane da tafiyar Arbaeen kuwa, Nawab ya ce: Akwai tattaki guda 25 a duniya, daya daga cikinsu shi ne tattakin Arbaeen. Wasu hanyoyin suna da tsawon kilomita dubu, wasu kuma suna cike duwatsu fako da kayoyi ne, wasu kuma suna tafiya kamar akan kirjinsu, amma babu daya daga cikinsu da za a iya kwatantataw da tafiyar Arbaeen. A wasu tattakin, ba zaka samu anayin hidima ga wasu ba; wanda hakan ke nuna yana matuƙar banbanci sosai da ma'anar tafiyar Arbaeen.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da bayanin mataki na biyu na Jagoran juyin juya halin Musulunci, wakilin Jagoran a harkokin Hajji da Ziyara ya kara da cewa: Ya yi wasiyoyi guda bakwai wadanda daya daga cikinsu ita ce salon rayuwa; salon rayuwa shine matakin gaske don ingantacciyar rayuwa. Haka nan maganar Imam Husaini (AS) tana da kyawawan batutuwa a fagen salon rayuwa. Ciki har da gyarawa da haɓaka kai da ƙoƙari don godiya ga niimomin Allah, wanda hakan ke sanya kuzari mai kyau ga wasu.
Nawab ya ci gaba da cewa: Imam Husaini (AS) ya ce: Ku sani su bukatun mutane a gare ku ni'imomi ne daga ni'imomin Ubangiji, kuma godiya ga wannan ni'ima dole ne. Kyawawan ayyuka suna da kyau, kuma aikata su shine biyan bukatun al'ummar yau. Haka nan, tare da yin kokari da yafiya, mutum na iya kaiwa wani matsayi mai girma; Ya kamata a yi afuwa ko ga wadanda ba su da fatan samunta. Hakanan ya kamata a yi amfani da iko don taimakawa wasu.
Wakilin Jagora mai kula da harkokin Hajji da Ziyara ya yi ishara da muhimmancin haduwa da hadin kai a tsakanin al'umma inda ya ce: A yau al'ummarmu na bukatar haduwa cikin gaggawa. Masu gujewa mutane su kulla hulɗa da gaggawa don taimaka wa wasu da niyyar kusantar juna da magance matsaloli.
A karshe ya jaddada cewa: Abubuwan da aka ambata daga cikin kalmomin Imam Husaini (AS) a cikin hudubarsa ga sahabbansa, dukkansu za su iya zama jagora ga aiki don bukatun al’umma a yau.
...........
Ƙarshen saƙo / 218
Your Comment