Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlulbayt (AS) - ABNA – ya habarta cewa: A cewar majiyoyin kasar Masar, adadin manyan motocin da suka shiga tun ranar Alhamis ya kai 161. A halin da ake ciki kuma, a wata hira da tashar Aljazeera Mohammed Abu Afesh daraktan kula da harkokin kiwon lafiya a Gaza, ya bayyana halin da ake ciki a fannin kiwon lafiya a matsayin abin damuwa matuka, ya kuma ce: “Muna cikin mataki na biyar na yunwa, kuma idan ba a kawo magunguna da kayan aikin jinya ba, rayukan da dama na cikin hadari.
Ya bayar da rahoton cewa, yara 17,000 ne ke fama da matsananciyar rashin abinci mai gina jiki, ya kuma bayyana tsananin karancin madara da fulawa da kayan aikin asibiti a matsayin mawuyacin hali. UNICEF ta sanar da cewa, a jiya (Asabar) manyan motocin dakon magunguna za su shiga Gaza.
Your Comment