Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya bayar da rahoto bisa nakalotowa daga Kamfanin dillancin labaran IRNA cewa: dubban al'ummar kasar Yemen ne suka gudanar da zanga-zanga a safiyar yau Juma'a a lardin Sa'ada (arewa) mai taken "Ba za mu lamunci kisan kiyashi a Gaza da kai wa al'ummarsu da wuraren masu tsarki hari ba".
Mahalarta muzaharar suna masu dauke da alluna, sun yi kira da a dage wannan kawanyar da kuma kawo karshen manufar kashe mata da kananan yara da ake zalunta a Gaza, tare da yin Allah wadai da hadin kai da shiru da kasashen duniya suke yi ga 'yan mamayan sahyoniyawa.
A jiya (Alhamis) Jami'ar San'a ta kasar Yemen ta gudanar da wata gagarumar zanga-zanga mai taken "Mun Tsaya Kyam Tare Da Gaza... mun tsaya kyam wajen fuskantar zaluncin yahudawan sahyoniya" wacce aka gudanar domin nuna hadin gwiwa da goyon bayan mazauna yankin Zirin Gaza a daidai lokacin da gwamnatin yahudawan sahyoniya ta kakaba mata takunkumin yunwa.
A wajen taron, mataimakin firaministan gwamnatin Sana'a Mohammed Miftah, ya dorawa Amurka cikakken alhakin yunwar da Falasdinawa ke fuskanta a Gaza, inda ya yaba da tsayin dakan da Al’ummar Gaza suka yi tare da jaddada cewa Gaza wata alama ce mai kima da ke nuna girman daukakar al'ummar kasar.
Shugabancin Jami'ar Sana'a ya kuma fitar da sanarwar cewa, inda ta bayyana cikakken goyon bayanta ga al'ummar Palasdinu, tare da yin kira ga 'yantattun mutane a duniya da su dauki matakin gaggawa don tallafawa Gaza da ke fuskantar yakin kisan kiyashi da yunwa.
Wannan dai shi ne karo na ba adadi da al'ummar kasar Yemen ke gudanar da zanga-zanga a sassa daban-daban na kasarsu domin nuna goyon bayansu ga Gaza tare da amincewa da matakin da sojojin kasarsu ke dauka kan makiya yahudawan sahyoniya da Amurka.
Sojojin Yaman sun yi alkawarin ci gaba da kai hare-hare kan jiragen ruwan Isra’ila ko na duk wata kasa da take tura jiragenta zuwa Isra’ila da yankunan da aka mamaye a cikin tekun bahar maliya har sai gwamnatin Isra'ila ta dakatar da kai hare-hare a Gaza.
Dakarun sojin Yaman sun jaddada cewa, zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigin tekun Aden da kuma tekun Bahru Maliya a saukake yake ga sauran jiragen ruwa kuma suna samun cikakken tsaro.
Your Comment